Friday, December 6
Shadow

Karya ake mana, bamu ce mun daina siyo man fetur daga kasar waje ba>>NNPCL

Kamfanin man fetur na kasa,NNPCL ya musanta Rahotannin dake cewa ya daina shigo da tataccen man fetur daga kasashen waje inda a yanzu yake sayen man daga matatar man fetur ta Dangote.

Labarai sun yadu dai cewa NNPCL tace ta daina shigowa da man fetur daga kasashen waje.

Saidai a sanarwar da kakakin NNPCL din Mr Femi Soneye ya fitar yace wannan rahoto ba gaskiya bane.

Yace suna dubawane su ga idan shigo da man fetur din daga kasar waje yafi sauki to daga wajen zasu siyo idan kuma sayenshi a gida yafi sauki to sai su siya a gida.

Yace lamarin labarin cewa sun daina shigo da man fetur ba gaskiya bane inda ya jawo hankalin ‘yan jarida da su rika yin bincike kamin watsa labaransu.

Karanta Wannan  Ƴan Najeriya sama da miliyan 28 ba sa mu'amulla da bankuna - CBN

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *