
Kasar Kazakhstan ta yi dokar haramta sanya Niqabi da duk wani abu me rufe fuska.
Shugaban kasar, Tokayev ne ya sakawa sabuwar dokar hannu wadda ta jawo cece-kuce da Allah wadai da bayyana cewa ta take hakkin mata musamman musulmi.
Dokar tace ana kokarin samar da tsaro ne a kasar sannan kuma saka Niqabi bakuwar al’adace a kasar.