
Kotun Magistrate dake Ago Iwoye, a jihar Ogun ta daure wani matashi me suna Adebanjo Segun dan kimanin shekaru 21 saboda satar kaza.
Kakakin Hukumar NSCDC na jihar, Dyke Ogbonnaya ne ya sanar da hakan a wata sanarwa daya fitar ranar Laraba.
Lamarin ya farune ranar Laraba, February 19, 2025 inda aka kama matashi Adebanjo.
Ogbonnaya ya bayyana cewa, Matashin ya taba aikata hakan a watan Disamba na shekarar 2024 amma aka yafe masa da tunanin cewa shine na farko da ya taba aikatawa.
Yace amma a wannan karin an gurfanar dashi a kotu inda kotun ta yanke masa hukuncin daurin watanni 6.