Monday, December 16
Shadow

Kwana nawa jinin haila yakeyi

Jinin Haila yanayin kwanaki 3 ne zuwa 8, amma da yawa jinin hailarsu yanayin kwanaki 5 Wanda hakan ba matsala bace.

Jinin yana zuba da yawa a kwanaki 2 na farko, sannan a kwanakin farko da kika fara jinin Al’ada, zaki iya ganin jini Pink, a yayin da ya kai kwanakin tsakiya, jinin zai iya komawa jaa, watau red, a yayin da yazo karshe, zai koma light Brown.

Idan kika gama jinin gaba daya, zaki ga farin ruwane kadai ke fita daga gabanki.

Idan kika yi kwanaki 90 ko watanni 3 baki ga jinin al’adarki ba kuma ba ciki kike dauke dashi ba, ba shayarwa kike ba, to ki gaggauta ganin likita.

Karanta Wannan  Jinin haila mai wasa

Saidai akwai abubuwan dake sa kwanakin jinin al’adarki su canja ko su rikice:

Yawan shekaru: Mace data fara manyanta zata iya ganin kwanakin jinin al’adarta sun ragu kuma tana yawan yin jinin al’adark akai-akai.

Amfani da magungunan tazarar Haihuwa: Wasu Magungunan tazarar Haihuwa na kawo rikicewar Al’ada.

Rashin Lafiya: Idan jinin al’adarki ya wuce kwanaki 7 a wani kaulin, kwanaki 8 ki gaggauta ganin likita, watakila rashin lafiyace kike fama da ita.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *