
Ma’aikatar ilimi ta tarayya, ta bayyana cewa, Ministan Ilimi, Tunji Alausa ya bada shawarar canja tsarin karatun Najeriya daga JSS da SSS zuwa shekaru 12 ne amma bai ce an canja ba.
Sanarwar tace maganar canja tsarin kai tsaye ba gaskiya bane.
Me magana da yawun ma’aikatar Ilimin, Folasade Boriowo ta bayyana cewa, kwamitin Ilimi na kasa zai duba wannan shawara kamin sanin matakin da ya kamata a dauka na gaba.
Ministan ya bayar da wannan shawara ne a Abuja ranar 6 ga watan Fabrairu a wajan wani taro kan Ilimi da aka yi a Abuja.