Monday, March 24
Shadow

An gurfanar da tsohon Minista kuma tsohon dan takarar shugaban kasa Kabiru Turaki a kotu bisa zargin yin lalata da wata mata har ta kai ga ya dirka mata ciki

Rahotanni daga babban birnin tarayya, Abuja na cewa, an gurfanar da tsohon Ministan ayyukan na musamman Kabiru Turaki (SAN) a kotun magistre dake Abuja bisa zargin yin lalata da wata mata.

Saidai Turaki ya musanta zargin da ake masa bayan da aka karanto masa zarge-zargen a gaban me shari’a, Abubakar Jega.

An zargi ministan da cewa a tsakanin watan Disamba na shekarar 2014 zuwa watan August na shekarar 2016 ya kai wata me suna  Ms. Hadiza Musa wani otal me suna Hans Palace inda yayi lalata da ita.

Ya kuma sake yin lalata da matar a otal din Ideal Home Holiday dake Asokoro tsakanin watan August 2016 zuwa watan November 2021.

Karanta Wannan  Bankin China ya bai wa Najeriya rancen kuɗin gina titin jirgi kasa daga Kano zuwa Kaduna

Daga baya ma sai ya kama mata gida dake da adireshin at No. 12 Clement Akpagbo Close, Gauzape inda ya ci gaba da lalata da ita da sunan cewa ya aureta.

A karshe dai ya dirka mata ciki har ta samu haihuwar diya mace.

Bayan data haihu, An zargi Turaki da yin garkuwa da matar da diyarta inda yayi mata barazanar yin amfani da karfinsa wajan kasheta ita da diyarta.

A karshe dai lauyan Turaki, A. I. Mohammed ya nemi kotu ta bayar da belinsa bisa alkawarin cewa duk sanda aka nemeshi zai bayyana a gaban kotun.

Mai shari’a Jega ya bayar da belin Turaki akan Naira Miliyan 1. Da kuma mutane 2 da zasu tsaya masa sannan ya saka ranar 11 ga watan Maris dan ci gaba da wannan shari’ar.

Karanta Wannan  Kalli hotunan motar Tesla Cybertruck ta Naira Miliyan 224 da mawaki Davido ya siya

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *