
Malam Ibrahim Mu’azzam dake fadakarwa a kafafen sada zumunta yayi sha’awar barin wa’azi ya koma Film bayan da ya ga an baiwa wata ‘yar Film kyautar Motar GLK.
Malam yace idan ya shiga film din wata kila shima a samu wani ya bashi kyautar motar, daga nan sai ya tuba ya koma ya ci gaba da wa’azin.
Saidai Da alama wannan magana yayi ta ne a matsayi shagube ko zunde.