Sunday, March 23
Shadow

Matatar Ɗangote ta sake rage farashin man fetur

Matatar Man Ɗangote ta sake rage farashin man fetur daga naira 890 a kan lita zuwa naira 825 – wato ragin naira 65 kenan a kan kowace lita ga ‘yan kasuwa.

A wata sanarwa da ta kamfanin ya fitar a yau Laraba, ya ce ragin zai fara aiki ne daga gobe Alhamis, 27 ga watan nan na Fabarairun 2025.

kamfanin ya ce ya yi haka ne domin sauƙaƙa wa al’umma Najeriya, yayin da suke shirin fara azumin watan Ramadana, tare kuma da tallafa wa shirin Shugaba Tinubu na neman farfaɗo da tattalin arziƙin ƙasar ta hanyar rage wa al’ummar ƙasar nauyin kuɗaɗe da ke kansu.

Karanta Wannan  Remi Tinubu da Ribadu za su jagoranci yi wa Najeriya addu'a dan ta fita daga matsalar tsananin Rayuwa

Wannan shi ne karo na biyu da matatar take rage farashin man fetur a watan na Fabarairun 2025, inda da farko ta yi ragin naira 60.

Haka kuma a watan Disamba na 2024 lokacin bikin Kirsimeti da sabuwar shekara, matatar ta rage farashin man fetur ɗin da naira 70.50, daga naira 970 zuwa 899.50 domin sauƙaƙa wa jama’a a cewar matatar.

A sanarwar kamfanin ya yi kira ga ‘yankasuwa masu sayar da man da su tallafa wa wannan yunƙurin nashi na rage wa ‘yan Najeriya wahala, su tabbatar al’umma ta amfana da wannan sauƙi.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *