
Babban Malamin addinin Islama a jihar Kaduna, Sheikh Musa Yusuf Asadussunnah ya soki yabon da akewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai da cewa shine zai ceto mutanen Arewa.
A cikin Tafsirinsa na Azumin watan Ramadana, Sheikh Musa yace a lokacin cutar Korona, duk Duniya babu inda aka matsawa mutane kamar jihar Kaduna.
Yace sai da aka kulle mutane aka hanasu yin Sallar Juma’a ta tsawon sati goma sha.
Yace irin wannan ne za’a ce wai shine zai ceto mutanen Arewa?
Malam ya kawo karin abubuwan da Tsohon Gwamnan Kadunan yayi irin su kara kudin makarantar jami’ar Jihar Kaduna, da Rushe-Rushen gidaje da sauransu.
Malam Nasiru Ahmad El-Rufai dai ya bar Jam’iyyar APC zuwa SDP inda yace ya dauri aniyar kwace mulki daga hannun APC a shekarar 2027.