
Karamin Ministan Tsaro, Bello Matawalle, ya yi tir da kalaman da tsohon minista kuma tsohon gwamnan Jihar Rivers, Rotimi Amaechi, ya yi kwanan nan.
Amaechi ya ce Shugaba Bola Tinubu da sauran ƴan siyasa ba za su mika mulki ga matasa ba tare da an kai ruwa rana ba.
A wata sanarwa da daraktan yada labarai na ma’aikatar tsaro, Henshaw Ogubike, ya fitar a jiya Alhamis, Matawalle ya bayyana kalaman Amaechi a matsayin “rura wutar rikici.”
“Abin takaici ne kuma babbar barazana ga kasa idan tsohon mai rike da mukamin gwamnati zai yi irin wadannan maganganu,” in ji sanarwar.
“A daidai lokacin da gwamnati ke aiki tukuru don inganta hadin kan kasa da tsaro, babu wani shugaba mai kishi da zai rura wutar tashin hankali da rikicin siyasa.”