Kowane tsakanin namiji da mace suna da sha’awa, saidai bisa al’ada akan ce sha’awar mace ta fi karfi amma ita kuyace ke hanata nunawa.
Bincike dai ya tabbatar da cewa, maza sun fi mata tunani akan jima’i,kuma sun fi mata neman yin jima’i, kuma sha’awarsu tafi sauri da saukin tashi fiye da ta mata.
A yayin da su kuma mata yanayin sha’awarsu abune me cike da rikitarwa.
Malami a jami’ar Indiana ta kasar Amurka, Justin Garcia, PhD, da kuma kwararriya me bayar da shawara kan rayuwar aure, Sarah Hunter Murray, PhD sun bayyana cewa, ba lallai a samu sakamako me kyau ba bayan yin binciken wa yafi karfin sha’awa tsakanin namiji da mace ba.
Dalilinsu kuwa shine yawanci maza sukan iya bayyana ra’ayinsu akan irin wannan zance amma mata ba kasafai sukan iya fadar abinda ke ransu ba game da karfin sha’awarsu, hakan kuwa ya samo asali ne daga al’ada da kuma addinin da mutum ya taso cikinsu.
Sannan babbar hanyar gano wannan amsa itace ta hanyar bincike amma shi kuma binciken idan an yishi, ba’a cika samun sakamako me gamsarwa ba saboda ana ganin wasu suna yin karya.
Dr. Murray tace abinda suka dauka shine cewa matsayin sha’awar mata da maza dayane, babu wanda yafi wani.
Bincike da yawa sun nuna wannan sakamako inda kuma bincike da yawa sun zo kankankan akan cewa matane suka karfin sha’awa wasu kuma su ce mazane suka fi karfin sha’awa.