Wednesday, October 9
Shadow

‘Muna fargabar barkewar cutuka masu muni a Maiduguri’

Masana harkokin lafiya a Najeriya sun yi kira ga gwamnatin kasar da ta aike da tawagar likitoci na musmaman da suka kware kan cututuka masu yaɗuwa zuwa Borno saboda fargabar barkewar cututuka sakamakon ambaliyar ruwan da aka fuskanta a jihar.

Masanan sun ce, suna fargabar barkewar cututuka irinsu zazzabin cizon sauro, da Zika, da zazzabin typoid, da na dange, da kuma uwa uba amai da gudawa, sakamakon irin dattin da ambaliyar ruwa ta kwaso da gawarwakin makabartu da ruwan ya dauko.

Dr Nasiru Sani Gwarzo, babban sakataren ma’aikatar Ilimi a Najeriya, kuma masani kan harkokin kiwon lafiya ya shaida wa BBC cewa, dole ne hukumomi su gaggauta shawo kan ruwan da ya malale asibitin koyarwa na Maiduguri saboda wasu daga cikin na’urorin asibitin akwai wadan ke da sinadarin nukiliya a ciki da ke da matukar hadari ga lafiyar al’umma.

Karanta Wannan  Akalla mutum 1,301 ne suka mutu a yayin aikin Hajjin bana – Saudi Arabia

Dr Gwarzo, ya ce “A hasashensu wato su masana kiwon lafiya suna ganin duk inda aka samu matsala ta ambaliyar ruwa to irin wadannan abubuwa da suka hadar da barkewar cutuka kan biyo baya.”

Ya ce, “Kamar yadda aka sani akwai manyan injina na kula da lafiya da ke babban asibitin koyarwa na Maiduguri da ke da sinadrin nukiliya a cikinsu ruwa ya taba su, a don haka ya kamata masu ruwa da tsaki a bangaren nukiliya a Najeriya su je suyi bincike a kan inda wannan ruwan daya shiga injinan da ke da nukiliya ya bi, da yadda za a killace ce, saboda ba za a ga barnar hakan ba sai nan da wasu shekaru masu yawa.”

Karanta Wannan  JARABTA: Cikin Kwanaki Uku A Jere, Ya Rasa Matarsa Da Yaransa Biyu

Masanin kiwon lafiyar, ya ce a yanzu kamar yadda hukumomi ke yi na kwashe jama’a daga inda za su iya fuskantar matsala mataki ne mai kyau, to amma yana da kyau a gaggauta samar musu da ruwan sha.

“Idan nace ruwan sha ina nufin tsaftatacce wanda bana garin ba, sannan a samar da wadataccen abinci, a inganta matsugunnin da za a tsugunnar da mutane.”

Dr Nasiru Gwarzo, ya ce, “Yana da kyau gwamnatin jihar Borno da ta tarayya su nemo irin masana kiwon lafiyarmu da aka bawa horo a game da yaki da annoba da kuma abubuwan da ke biyo bayanta kamar ta ambaliyar ruwa don ayi aiki da su a Maiduguri.”

Ya ce, su wadannan kwararrun za a shiga da su gari-gari da lungu da sako na wurin da aka samu ambaliyar don a wayarwa da mutane kai a game da abin da ya kamata su yi.

Karanta Wannan  NAFDAC ta yi gargaɗi kan amfani da sinadarin Sniper don taskance abinci

Birnin Maiduguri ya fuskanci mummunar ambaliyar ruwa sakamakon fashewar madatsar ruwa ta Alau, lamarin da ya haddasa ruwan ya malale dubban gudaje da makarantu da asibitoci da tituna da gine-ginen gwamnati da ma babban asibitin koyarwa na jihar da ma jami’ar jihar.

Bayanai sun ce lamarin ya fi muni a unguwannin Fori da Galtimari da Gwange da kuma Bulabulin.

Kazalika ambaliyar ambaliyar ta shafi gidan adana namun daji, lamarin da ya sa dabbobi suka fita kan titunan suna gararamba.

Ambaliyar dai ita ce mafi muni a jihar Borno cikin shekaru 30.

Leave a Reply

Your email address will not be published. Required fields are marked *