
Najeriya da Saudi Arabiyya sun sanya hannu kan wata yarjejeniyar fahimta domin karfafa yaki da hada-hadar kwayoyi.
A ranar Litinin Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta NDLEA ta Najeriya da kuma Hukumar da ke yaki da fataucin miyagun kwayoyi ta Saudiyya GDNC, suka sanya hannu kan yarjejeniyar a Riyadh.
Cikin wata sanarwar da daraktan yada labarai na hukumar ta NDLEA, Femi Babafemi, ya fitar ya ce kasashen biyu sun amince su kara karfafa yaki da fataucin miyagun kwayoyi a dukkan iyakokinsu.
Da ya ke magana a wajen sanya hannu kan yarjejeniyar, shugaban hukumar ta NDLEA, Birgediya Janar Buba Marwa, mai ritaya, ya ce dukkan kasashen sun jima suna yin hadaka da bangarori daban daban.
Marwa, wanda ya samu rakiyar darakta a sashen bincike da gudanarwa na hukumar, Ahmed Ningi, ya ce dukkan kasashen na da kyakkyawar alaka a tarihi.
Ya ce,” A yau rana ce ta musamman mai matukar muhimmanci ga dukkan kasashen biyu.”
” Yau rana ce da ta kara kyakkyawar dangantaka tsakanin kasashen biyu, musamman hukumomin da ke yaki da ta’ammali da miyagun kwayoyi.” in ji Marwa.
Da ya ke bayani a game da muhimmancin yarjejeniyar, Marwa, ya ce hada-hadar da miyagun kwayoyi ta zamo babban kalubale a duniya wanda ke bukatar daukar kwakkwaran mataki.
Ya ce a duk inda ake ta’ammali da kwayoyin masu illa to akwai babbar barazana ga al’ummar da ke wajen.