Obasanjo Ya Ziyarci Uwargidan Shugaban Kasa Bayan ‘Yan Kwanaki An Hange Shi Sanye Da Hula Kalar Tambarin Tinubu
Obasanjo Ya Ziyarci Uwargidan Shugaban Kasa Bayan 'Yan Kwanaki An Hange Shi Sanye Da Hula Kalar Tambarin Tinubu
Tsohon shugaban kasa Olusegun Obasanjo ya ziyarci uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu domin murnar bikin Sallah, ranar Litinin a Legas.
Mataimaki na musamman ga uwargidan shugaban kasa kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Busola Kukoyi, ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X tsohon shafin twitter.
Ziyarar ta zo ne kwanaki bayan da aka ga tsohon shugaban kasar a wani taron sanye da hula da kayan adon da ya yi kama da tambarin da ke kan hular Tinubu.
Wannan ci gaban ya haifar da martani daban-daban, yayin da wasu 'yan Najeriya ke tunanin ko Obasanjo ya koma goyon bayan Tinubu.
A ci gaban zaben 2023, Obasanjo ya amince da Peter ...





