Thursday, January 8
Shadow
An dauke Wuta a wani sashe na kasar Amurka inda sama da mutane 300,000 suka fada Duhu

An dauke Wuta a wani sashe na kasar Amurka inda sama da mutane 300,000 suka fada Duhu

Duk Labarai
Rahotanni daga kasar Amurka na cewa, an dauke wutar lantarki a kasar wanda ya jefa mutane 350,000 cikin Duhu. Lamarin ya farune dalilin ruwa me tsanani da iska da aka yi a yankin Michigan. Mahukunta sun yi gargadin cewa, mutane su kiyaye akwai yiyuwar ci gaba da ruwan da kankara. Saidai wannan labarin yasa hukumar kula da wutar lantarki mamaki, inda har suka saka alamar ido a bude sosai a kafar X, watau Alamar abin ya basu mamaki kenan. Da yawan 'yan Najeriya sun ji haushin wannan lamarin inda suke cewa ai dauke wutar ba irin na Najeriya bane da ake yi kullun. https://twitter.com/i/status/2007087923242443090
Da Duminsa: Sabbin Bayanai sun fito game da shirin komawar Gwamna Abba Jam’iyyar APC

Da Duminsa: Sabbin Bayanai sun fito game da shirin komawar Gwamna Abba Jam’iyyar APC

Duk Labarai
Rahotonni nata kara karfi kan shirin komawar Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf jam'iyyar APC. Sabbin Rahotannin da ake samu shine cewa nan da ranar Litinin in Allah ya kaimu, Gwamna Abba Kabir Yusuf a hukumance zai koma jam'iyyar APC. Hakan na zuwane yayin da siyasar Kano ke ci gaba da daukar Dumi. Ana ganin wannan komawar ta Gwamna Abba jam'iyyar APC zata iya kawo baraka tsakaninsa da Dr. Rabiu Musa Kwankwaso.
Kalli Bidiyon abinda wani dan Kungiyar Kwallon Kafa ta Al Ahli yawa Ronaldo a filin wasa da ya baiwa Ronaldon Haushi

Kalli Bidiyon abinda wani dan Kungiyar Kwallon Kafa ta Al Ahli yawa Ronaldo a filin wasa da ya baiwa Ronaldon Haushi

Duk Labarai
Bayan wasan da aka buga tsakanin Al Ahli da Alnasr da aka tashi Al Ahli ta yi nasara da 3-2, wani abu ya faru tsakanin Ronaldo da wani ma'aikacin Kungiyar ta Al Ahli. Yayin da Ronaldo ya ke fita daga filin wasan, ma'aikacin kungiyar Al Ahli, ya zo ya wuceshi yana fadar Messi, Messi. Abin yawa Ronaldo Haushi, har sai da Ronaldon ya je ya sameshi. Lamarin ya dauki hankula sosai. https://twitter.com/i/status/2007178627436437564
Na baku kwana 3, ko dai ku sakeni, ko kuma zaku nenemi ku rasa>>Faston nan na asar Ghana da yace za’a yi tashin Qiyama ranar Kirsimeti amma ba’a yi ba

Na baku kwana 3, ko dai ku sakeni, ko kuma zaku nenemi ku rasa>>Faston nan na asar Ghana da yace za’a yi tashin Qiyama ranar Kirsimeti amma ba’a yi ba

Duk Labarai
Fasto Ebo Noah wanda ya ce wai an masa wahayi za'a yi tashin Qiyama ranar Kirsimeti, 25 ga watan Disamba amma ba'ayi ba, ya gargadi hukumomin kasar Ghana da suka kamashi. Faston dai an kamashine saboda wannan abu da yayi ya dauki hankulan Duniya. Saidai ya gargadi hukumomin kasar Ghana da cewa ya basu kwanaki 3 ko dai su sakeshi ko ya bace daga gidan yarin da ake tsare dashi.
Kalli Bidiyon: Magoya bayan Kungiyar Kwallon kafa na kasar Senegal na ta shan Yabo saboda yanda suka tsaya bayan kammala wasa suka share filin wasan

Kalli Bidiyon: Magoya bayan Kungiyar Kwallon kafa na kasar Senegal na ta shan Yabo saboda yanda suka tsaya bayan kammala wasa suka share filin wasan

Duk Labarai
Magoya bayan kungiyar kwallon kafa na kasar Senegal sun tsaya bayan an kammala wasa suka share filin tas. Hakan ya jawo musu yabo sosai da wannan hali na tsafta da suka nuna. https://twitter.com/i/status/2007138542506725416 A gasar cin kofin Duniya, magoya bayan kwallon kafa na kasar Japan sun rika yin irin wannan abu. A jiya ne dai Hutudole ya kawo muku cewa suma 'yan kwallon kafar na kasar Senegal sun dauki hankula bayan da aka gansu sun tafi yin Sallar Juma'a.
Allah Sarki: Kalli Bidiyon yanda Dan Danben Najeriya, Anthony Joshua yake sauraren Qur’ani kamin Khàdàrìn da ya rutsa dashi da abokansa

Allah Sarki: Kalli Bidiyon yanda Dan Danben Najeriya, Anthony Joshua yake sauraren Qur’ani kamin Khàdàrìn da ya rutsa dashi da abokansa

Duk Labarai
An ga Anthony Joshua yana sauraren Qur'ani a cikin mota kamin Hadarin motar da ya rutsa dashi da abokansa. An ji yana cewa, yana rokon Allah ya taimakeshi, ya bashi nasara ya kuma daukakashi. https://twitter.com/i/status/2007203246549721523 Anthony Joshua da abokansa sun yi Khàdàrì inda abokan nasa biyu suka rigamu gidan gaskiya amma shi ya ji rauni. Tuni dai an sallameshi daga Asibiti.
Shugaban kasar Mozambique ya yiwa ‘yan kwallon kasarsa Alkawarin Naira Miliyan 11.3 kowanensu idan suka yi nasara akan Najeriya

Shugaban kasar Mozambique ya yiwa ‘yan kwallon kasarsa Alkawarin Naira Miliyan 11.3 kowanensu idan suka yi nasara akan Najeriya

Duk Labarai
Shugaban kasar Mozambique ya yiwa 'yan Kwallonsa Alkawarin cewa idan suka yi nasara a wasan Da zasu Buga da Najeriya zai baiwa kowannensu Kyautar Naira Miliyan 11.3 kowannensu. A ranar Litinin ne Najeriya zata buga wasa da kasar Mozambique a ci gaba da kasar cin kofin Afrika na AFCON da ake bugawa a kasar Morocco.
Harajin da Gwamnatin tarayya zata fara karba Damfara ce>>Inji Peter Obi

Harajin da Gwamnatin tarayya zata fara karba Damfara ce>>Inji Peter Obi

Duk Labarai
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar Labour Party a zaben shekarar 2023, Peter Obi ya bayyana cewa, Harajin da Gwamnatin tarayya zata fara karba a hannun Talakawa Damfara ne. Ya bayyana cewa, Har 'yan majalisa sun bayyana cewa dokar da aka wallafa ba wadda suka amince da ita bace amma duk da haka gwamnatin ta yi gaban kanta tace sai ta karbi Haraji. Yace Harajin zai kara Jefa 'yan Najeriyar da yawa cikin Talauci ne. Yace kuma ba da karbar Haraji ake ciyar da kasa gaba ba inda yace, ana ciyar da kasa gaba ne ta hanyar azurta 'yan kasa ta hanyar baiwa kananan masana'antu damar fadada kasuwancinsu da sauran abubuwan karfafa tattalin arziki.