Thursday, September 17
Shadow
Kalli Bidiyon: Rawar Badala da  ‘yan Mata suka yi a wajan Show din Otega ta jawo Allah wadai

Kalli Bidiyon: Rawar Badala da ‘yan Mata suka yi a wajan Show din Otega ta jawo Allah wadai

Duk Labarai
'Yan mata sun yi rawar rashin tarbiyya da bada a wajan show din Otega wanda Bidiyon rawar ya karade kafafen sada zumunta. Da yawa sun rika Allah wadai da lamarin inda ake ta tattauna yanda rashin Tarbiyya tsakanin matasan Arewa ke kara kamari. https://www.tiktok.com/@danyahuza/video/7682457225515814164?_r=1&_t=ZS-99WlEcZtm2W https://www.tiktok.com/@diamond_events.ng/video/7682222461944958226?_r=1&_t=ZS-99Wko9ao7OP https://www.tiktok.com/@amstudio78/video/7682143289952193812?_r=1&_t=ZS-99WlLgGEQq5
Sukar da ake min kan riddar da dana yayi ka iya sa in bar Musulunci>>Inji Sheikh Nura Khalid

Sukar da ake min kan riddar da dana yayi ka iya sa in bar Musulunci>>Inji Sheikh Nura Khalid

Duk Labarai
A martanin da yake yi ga masu sukarsa kan komawar dansa Kirista, Sheikh Nura Khalid, Digital Imam ya bayyana cewa, wasu ma cewa suka yi dama shine ya zama Kiristan. Yace yanzu da yayi fushi a zama Kirista wace riba aka samu? Yace in banda Allah ya taimakeshi yayi zurfi a Ilimin Addinin Musulunci? https://www.tiktok.com/@shaaweuei5p/video/7682374744993205524?_r=1&_t=ZS-99WiImehRvo
Wanda suka je wajan Taron APC a Kano sun ce dubu 3 aka basu, kuma daga yau sun bar APC

Wanda suka je wajan Taron APC a Kano sun ce dubu 3 aka basu, kuma daga yau sun bar APC

Duk Labarai
Wannan wasu ne daga cikin wadanda suka je wajan taron kaddamar da fara yiwa shugaba Tinubu ya kin neman zabe a jihar Kano. Sunce sun kashe sama da dubu ukku kowannensu wajan hidimar zuwa wajan taron siyasar daga Aljihunsu. Amma da aka tashi sallamarsu aka ba kowannensu dubu hudu, ko kudin motarsu da hidimar da suka yi ta zuwa wajan taron basu mayar ba. Sunce indai tafiyar APC haka take, to ba zasu yi ba. https://twitter.com/SamuelOmogor/status/2096710057979216355
Kalli Bidiyon: Addu’ar da Alaramma Ahmad Sulaiman yawa Gwamnan Kano a wajan taron fara yiwa Tinubu yakin neman zabe ta dauki hankula

Kalli Bidiyon: Addu’ar da Alaramma Ahmad Sulaiman yawa Gwamnan Kano a wajan taron fara yiwa Tinubu yakin neman zabe ta dauki hankula

Duk Labarai
Alaramma Ahmad Sulaiman ya dauki hankula a kafafen sada zumunta biyo bayan Bidiyonsa da aka gani yanawa Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf Addu'ar zarcewa a 2027. Ahmad Sulaiman yayi wannan addu'a ne a wajan taron fara yiwa gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf yakin neman zabe. https://www.tiktok.com/@mr__clown_/video/7682115257803771154?_r=1&_t=ZS-99W5G8z8poS
Kalli Bidiyon: Hukumar Hisbah ta kama matashiya saboda Bidiyon badala

Kalli Bidiyon: Hukumar Hisbah ta kama matashiya saboda Bidiyon badala

Duk Labarai
Hukumar Hisbah a jihar Kano ta kama wata matashiya me shekaru 18 saboda Bidiyon badala da ta yi wanda ya watsu sosai. Matashiyar tace ta je Kano daga jihar Adamawa ne dan ta shiga Harkar fim inda tace sanadiyyar hakan ne ta hadu da wasu matasa suka rika Bidiyon badala wanda ya watsu sosai a kafafen sada zumunta. Shima wanda suka yi Bidiyon tare an kamoshi ya bayyana nadamar abinda ya aikata. https://twitter.com/KafinHausaa/status/2096198859839922289