Idan mutum na son cin abinci me rai da lafiya sai ya kashe Naira 1,050 a kowace rana>>Inji Gwamnatin Tarayya
Hukumar Kula da gididdiga ta kasa NBS ta bayyana cewa kudin da mutum zai kashe ya ci abinci me gina jiki a Najeriya ya kai Naira 1,050 a kullun.
NBS ta bayyana hakane a wani rahoto data fitar ranar Laraba akan farashin abinci me gina jiki.
Tace a watan Maris, Naira 982 ake kashewa wajan cin abinci me gina jiki yayin da a watan Afrilu ya karu zuwa Naira 1,050.
NBS tace wannan farashin abincine da bashi da tsada wanda kuma ake samunsa a gida Najeriya amma kuma yana da duk sinadaran da Duniya ta yadda dasu na gina jiki.
Yayin da hukumar ta fitar da kudin da ake kashewa wajan cin abinci me gina jiki a kowane bangare na Najeriya, tace bangaren Arewa maso yamma nan ne ake kashe kudi mafiya karanci wanda suka kai Naira 781 wajan cin abinci me gina jiki a kullun.
Jihohin Kudu m...