Monday, December 15
Shadow
Yayin da Gwamnatin Tarayya tace Karyace, Kungiyar kiristocin Najeriya, CAN tace maganar da Amurka ta yi na cewa ana shekye kiristoci da yawa a Najeriya gaskiyane

Yayin da Gwamnatin Tarayya tace Karyace, Kungiyar kiristocin Najeriya, CAN tace maganar da Amurka ta yi na cewa ana shekye kiristoci da yawa a Najeriya gaskiyane

Duk Labarai
Kungiyar kiristocin Najeriya, CAN ta goyi bayan kasar Amurka da ta ce ana kashe kiristoci a Najeriya da yawa. Shugaban CAN, Archbishop Daniel Okoh ne ya bayyana hakan ranar Laraba. Yace kin fadawa kai gaskiya da zargi ba zai kawo karshen matsalar ba Yace karfin hali da fuskantar matsalar tare ne zai kawo yadda da juna a tsakani. Yace tabbas Kiristoci a sassa daban-daban na Najeriya musamman yankunan Arewa na fuskantar Kisa da asarar Dukiyoyi da sauransu. Sanatan kasar Amurka, Ted Cruz ne ya bayyana hakan inda yayi zargin cewa an kashe Kiristoci 52,000 da kona coci-coci 20,000 a Najeriya. Gwamnatin Tarayya dai Tuni ta karyata wannan ikirarin na satan kasar Amurkar.
Kwana daya bayan da Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya jinjinawa Gwamnatin Tinubu bisa farfado da tattalin arzikin Najeriya, Bankin Duniya yace duk da kokarin Gwamnati na farfado da tattalin arzikin, Mutane Miliyan 139 ne suka tsunduma cikin bakin Talauci a Najeriya

Bankin Duniya wanda shine gaba-gaba wajan baiwa Najeriya bashi yace mutane Miliyan 139 sun tsunduma cikin bakin Talauci a Najeriya. Bankin yace hakan na zuwane duk da ikirarin da Gwamnatin tarayya ke yi na cewa an samu habakar tattalin arziki. Bankin yace Gwamnatin sai ta kara himma wajan tabbatar da cewa Talaka na shaida wannan habakar tattalin arzikin da ake cewa an samu idan ana son a ga canji. Daraktan Bankin Duniya a Najeriya, Mathew Varghis ne ya bayyana hakan ranar Laraba a Abuja wajan taron bayyana ci gaban da aka samu. Ya jinjinawa Gwamnatin tarayya bisa ga cire tallafin man fetur da daidaita chanjin Naira zuwa kudaden kasashen waje wanda yace hakan matakai ne da zasu zama ginshikai wajan ci gaban Najeriya. Wannan bayani na bankin Duniya na zuwane kwana daya baya...
Kalli Bidiyo: Abubuwa na ci gaba da kankama a shirin sabuwar wakar Soja Boy wadda yake yi da Tsohuwar me saka Hijabi, Iftihal Madaki

Kalli Bidiyo: Abubuwa na ci gaba da kankama a shirin sabuwar wakar Soja Boy wadda yake yi da Tsohuwar me saka Hijabi, Iftihal Madaki

Duk Labarai
Tauraron me wakokin batsa na Arewacin Najeriya, Soja Boy na ci gaba da daukar Bidiyon sabuwar wakar sa wadda yake yi da Iftihal Madaki wadda aka saba gani da Hijabi a baya. Bidiyon da Soja Boy da Iftihal Madaki ke sakawa a shafukansu na sada zumunta na ci gaba da daukar hankula sosai. https://www.tiktok.com/@officialsojaboyy/video/7558963301598727432?_t=ZS-90OmmeoEiFF&_r=1 Kalli Bidiyon anan A baya dai Iftihal Madaki ta dauki hankula bayan da aka ganta a wata waka tana rawa da ba'a saba ganin tana yin irinta ba. Saidai a karo na biyu gashi an sake ganinta a Bidiyon wakar Soja Boy.
Ji yanda aka kama wani Barawon waya da ya sace wayar wata mata tana bacci amma bai kashe wayar ba, data kira yace sai ta bashi dubu 50

Ji yanda aka kama wani Barawon waya da ya sace wayar wata mata tana bacci amma bai kashe wayar ba, data kira yace sai ta bashi dubu 50

Duk Labarai
Wani barawo ya sace wayar wata mata yayin da take tsaka da bacci. Saidai be kashe wayar ba. Da me wayar ta kira, sai yace zai bata amma sai ta bashi dubu hamsin. Saidai tace masa bata da Dubu 50. Amma tace idan yana so zata bashi kanta. Aikuwa sai ya yadda. Tuni dai an kamashi, lamarin ya farune a Ikotun, dake jihar Lagos. https://twitter.com/stilldey4u/status/1975825042433790433?t=BKJonJHQDeI_6w3vR9tCJg&s=19
Kalli Bidiyo: Ana ci gaba da daukar sabuwar wakar Soja Boy inda aka ga Bidiyo yana kama Khugun Iftihal Madaki wadda a baya aka saba ganinta da Hijabi

Kalli Bidiyo: Ana ci gaba da daukar sabuwar wakar Soja Boy inda aka ga Bidiyo yana kama Khugun Iftihal Madaki wadda a baya aka saba ganinta da Hijabi

Duk Labarai
Ana ci gaba da daukar Bidiyon sabuwar wakar Soja Boy wadda suka yi Bidiyon ta tare da iftihal Madaki wadda a baya aka saba ganinta sanye da Hijabi a Bidiyon ta. A Bidiyon an ga yanda Soja Boy ya kamo Kugun Iftihal yayin da take sanye da doguwar bakar Riga. A wakar da suka yi da ita ta farko, Iftihal ta jawo cece-kuce sosai bayan ganinta tana rawa ba Hijabi. https://www.tiktok.com/@bigdoxxx/video/7558599404547083536?_t=ZS-90NSeHnCzIX&_r=1
Kalli Bidiyo: Wasannan na Mari da ake ganin Turawa na yi ya shigo Najeriya

Kalli Bidiyo: Wasannan na Mari da ake ganin Turawa na yi ya shigo Najeriya

Duk Labarai
Wasan Mari da mafi yawanci ake ganin Turawa na yi ya shigo Najeriya. Wasan wanda har ana saka kyauta ga wanda yafi iya yin marin an ganshi an fara yinshi a Najeriya. Lamarin dai ya baiwa mutane mamaki sosai inda ake ta muhawara akai. https://twitter.com/AsakyGRN/status/1975275774308663458?t=zMzci2-c8sk72ZCDflhcJw&s=19 Tuni dai wani malamin Addinin Islama ya jawo hankalin Musulmai da cewa wasan bai halasta ba a Musulunci kuma su gujeshi. https://twitter.com/IdrisAOni1/status/1975585618076774801?t=JQQfXTWH2WuPWr4dwZuinw&s=19
Kudi sun yi yawa a hannun mutane, Kuma na ji dadin matakan da CBN ya dauka wajan rage yawan kudaden dake hannun mutane>>Inji Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II

Kudi sun yi yawa a hannun mutane, Kuma na ji dadin matakan da CBN ya dauka wajan rage yawan kudaden dake hannun mutane>>Inji Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II

Duk Labarai
Me martaba sarkin Kano, Muhammad Sanusi II ya bayyana jin dadinsa game da matakan da babban bankin Najeriya CBN ya dauka wajan magance yawan kudi a hannun mutane. Sarki Sanusi yace hakan yasa hauhawar farashin kayan abinci ya ragu duk da dai har yanzu yana kan maki 20 wanda yayi yawa. Sarkin yace tattalin arzikin Najeriya ya dawo daga hanyar rugujewa da ya dauka saboda wanan mataki da CBN ya daka. https://twitter.com/KanEmirateMedia/status/1975645093714665940?t=wj0dZ4XwsPxOAD9AaX2o3A&s=19
Kalli Bidiyo: Wallahi da wadanda ba musulmai bane suka yi irin wannan Kalamai akan Janibin Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) da Musulmai sun turasu Qiyama>>Inji Farfesa Ibrahim Maqari

Kalli Bidiyo: Wallahi da wadanda ba musulmai bane suka yi irin wannan Kalamai akan Janibin Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) da Musulmai sun turasu Qiyama>>Inji Farfesa Ibrahim Maqari

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama Sheikh Farfesa Ibrahim Maqari Ya bayyana cewa, da wadanda ba musulmai bane suka yi kalamai na taba Janibin Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) yace da tuni hakan ya kawo tashin hankali. Malam yace "Da Tuni an fara Qone-Qone da an fhille Mhusu Khawuna. Yace amma wadanda suke kiran kansu musulmai ne ke irin wannan abin. Malam ya bayyana hakane cikin sheshekar kuka a wani Bidiyonsa da ya watsu sosai. https://www.tiktok.com/@hassan.a.hassan.2/video/7557739024941600011?_t=ZS-90N9J038S1p&_r=1
Ina mamakin yanda ake mana Qazafin wai muna Lalata da Mhata, Saboda matan dake bin mu mun yi ‘ya’ya da jikoki dasu>>Inji Tanimu Akawu

Ina mamakin yanda ake mana Qazafin wai muna Lalata da Mhata, Saboda matan dake bin mu mun yi ‘ya’ya da jikoki dasu>>Inji Tanimu Akawu

Duk Labarai
Tauraron Fina-finan Hausa, Tanimu akawu ya bayyana cewa, Abin na bashi mamaki wai da ake musu Qazafin cewa, suna lalata da mata. Yace yawanci matan dake binsu sun yi 'ya'ya da jikoki dasu. Yace dan fim me taimako ne inda yace shi kanshi ya aurar da yaran mutane 2. https://www.tiktok.com/@abdulsauty1/video/7558205933583617298?_t=ZS-90N7paOSItN&_r=1 Tanimu Akawu ya kawo misalin yanda wata yarinya bafulatana da akawa auren dole ta gudo ta sameshi tace tana son shiga film inda yace sai da ya kira iyayenta. Yace da Kano ta je da an lalata mata rayuwa.