Monday, December 15
Shadow
Ministan kimiyya da fasaha na Najeriya ya yi murabus kan zarginsa da amfani da digirin bogi

Ministan kimiyya da fasaha na Najeriya ya yi murabus kan zarginsa da amfani da digirin bogi

Duk Labarai
Shugaban Najeriya Bola Tinubu ya amince da murabus ɗin ministan kimiyya da fasaha na Najeriya Geoffrey Uche Nnaji. A wata sanarwa da mai magana da yawun shugaban Najeriya Bayo Onanuga ya fitar, ya ce shugaban ya amince da murabus ɗin ministan, wanda ya biyo bayan zarginsa da aka yi da amfani da digirin bogi. An dai zargi tsohon minista ne da amfani da digirin bogi daga Jami'ar Najeriya ta Nsuka, lamarin da ya ja hankalin ƴan ƙasar matuƙa, duk da ya musanta. Njaji ya ce ana masa bita da ƙulli ne, lamarin da ya zargi "abokan hamayyarsa a siyasa" da yunƙurin ɓata masa suna. Tinubu ya yi godiya a gare shi "bisa hidimta wa Najariya" sannan ya yi masa fatan alheri.
Kalli Bidiyon: A tabbatar malaman da aka gayyato zasu yiwa Malam Lawal Triumph Tambayoyi sun san Hadisi da Qur’ani sosai, idan ba haka ba zamu ji Kunya>>Inji Dan Darika Umar

Kalli Bidiyon: A tabbatar malaman da aka gayyato zasu yiwa Malam Lawal Triumph Tambayoyi sun san Hadisi da Qur’ani sosai, idan ba haka ba zamu ji Kunya>>Inji Dan Darika Umar

Duk Labarai
Dan Darika, Umar ya bayyana damuwa da kuma gargadi kan cewa ya kamata a ce an samu malamai wanda suka san Qur'ani da kuma Hadisi su zaina da malam Lawal Triumph. Umar yayi gargadin cewa, idan ba'a samu malamai masu ilimi ba, za'a iya jin kunya. Ya bayyana cewa ya san Malam Lawal Triumph sosai. https://www.tiktok.com/@umarpitykhalid0/video/7557750978754202898?_t=ZS-90LupEEOg53&_r=1
CBN sun saka sabuwar dokar kayyade hadahadar kudi na POS kada ya wuce Naira Miliyan 1.2 a rana

CBN sun saka sabuwar dokar kayyade hadahadar kudi na POS kada ya wuce Naira Miliyan 1.2 a rana

Duk Labarai
Babban bankin Najeriya, CBN ya saka sabbin dokokin hadahadar kudi na POS. CBN ya bayyana sabbin dokokin wanda yade dolene kowa da lamarin ya shafa ya tabbatar yana wa dokokin Biyayya. Daya daga cikin dokokin da suka fi daukar hankali itace wadda tace a kullun an Amincewa dan POS ne yayi hadahadar kudi da bata wuce Naira Miliyan 1.2 ba. Wasu dai na ganin wannan doka da wuya ta yi aiki domin mutum daya zai iya mallakar POS daban-daban fiye da daya.
Dangote ya rage farashin Gas din Girki

Dangote ya rage farashin Gas din Girki

Duk Labarai
Matatar Man fetur ta Dangote ta rage farashin Man Fetur. A yanzu farashin yana akan Naira ₦760 ne kan kowane kilo maimakon Naira ₦810 da ake saye a baya. Sauran masu samar da gas din girki a Najeriya irin su Matrix da Ardova suna sayar da gas dinne akan farashin Naira ₦920 Su kuwa AY Shafa da NIPCO suna sayar da gas dinne akan farashin Naira ₦910. Su kuwa Stockgap Depot suna sayar da gas dinne a farashi Naira ₦950 kan kowacce Lita. Hakan ya bayyana cewa, Gas din Dangote shine mafi Arha a Najeriya. Ana ganin hakan zai iya tilasta sauran masu samar da gas a Najeriya suma su rage farashinsu.
Ji yanda Matar soja Lt. Samson Haruna ta aikashi Qiyama ta hanyar Babbaqeshi Qurmus

Ji yanda Matar soja Lt. Samson Haruna ta aikashi Qiyama ta hanyar Babbaqeshi Qurmus

Duk Labarai
Matar sojan Najeriya Lt. Samson Haruna ta kasheshi ta hanayar cimma nasa wuta bayan da fada ya kaure tsakaninsu. Lamarin ya farune a Bassey Barracks, dake Ibagwa, karamar hukumar Abak dake jihar Akwa-Ibom. Lamarin ya farune ranar Sept. 22, 2025. Sojan wanda likita ne, sun samu zazzafar muhawara da matarsa me suna Mrs. Samson Haruna wanda hakan yasa ta yi amfani da fetur ta babbakeshi. Sojan ya samu raukuna sosai inda nan da nan aka garzaya dashi zuwa Asibiti. Bayan da aka je Asibitin ya rasu acan. An kama matar inda yanzu haka ake kan bicikenta.
Kalli Bidiyon: An yaye jami’an tsaro na musamman guda 380 da za su yi yaki da masu kwacen waya a Kano

Kalli Bidiyon: An yaye jami’an tsaro na musamman guda 380 da za su yi yaki da masu kwacen waya a Kano

Duk Labarai
An kammala horaswa da kuma yaye jami'an hukumar KOSSAP da aka samar na musamman a jihar Kano da zasu rika yaki da kwacen waya. Jami'an su 380 an kammala yaye su ne a ranar Lahadi inda kuma zasu fara aiki nan ba da jimawa ba. An shafe sati biyu ana basu horo. Matsalar kwacen waya yayi kamari a jihar Kano inda ake kashe mutane ana kwace musu wayoyi.
Lauya ya garzaya kotu inda yake neman ta hana Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan tsayawa takarar shugaban kasa a 2027

Lauya ya garzaya kotu inda yake neman ta hana Tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan tsayawa takarar shugaban kasa a 2027

Duk Labarai
Wani lauya me suna Johnmary JideObi ya shigar da karar tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan kan neman kotu ta hanashi tsayawa takarar shugaban kasa a 2027. Ya shigar da karar ne ranar Litinin a babbar kotun tarayya dake Abuja. Yace idan Goodluck Jonathan ya sake cin zabe zai yi shekaru fiye da 8 da doka ta yadda kowane shugaba yayi. Dan hakane yake neman a hanashi tsayawa takarar shugaban kasa a 2027.