Thursday, May 7
Shadow
Abin Kunya: ‘Yan Kwallon Najeriya, Super Eagles sun ce ba zasu je buga wasan su da Algeria ba idan ba’a biyasu hakkokinsu ba

Abin Kunya: ‘Yan Kwallon Najeriya, Super Eagles sun ce ba zasu je buga wasan su da Algeria ba idan ba’a biyasu hakkokinsu ba

Duk Labarai
Kungiyar 'yan kwallon Najeriya ta Super Eagles da masu horas dasu sun ce ba zasu je wasan da zasu buga da Algeria ba idan ba'a biyasu hakkokinsu ba. Kungiyar ta bayyana cewa akwai alkawuran kudaden da aka musu idan suka yi nasara a wasanni da kasashen Tanzania, Tunisia, Uganda, da Mozambique amma ba a cika musu wadannan alkawuran ba. Kungiyar tace ba zata ke garin Marrakech ba ranar Alhamis dan yin Atisayen wasan da zasu buga da kungiyar kasar Algeria ba idan ba'a biyasu ba. Najeriya dai zata yi wasan Quarter finals da kasar Algeria.
Kalli Bidiyon: Ni kirista ne amma na zama Musulmi

Kalli Bidiyon: Ni kirista ne amma na zama Musulmi

Duk Labarai
Wannan Kiristan ya bayyana cewa, ya Musulunta, saidai yace shi mawaki ne Yace babban dalilinsa na komawa Musulmi shine dan wakarsa ta samu daukaka. https://www.tiktok.com/@funnyalpha/video/7592315088418229524?_r=1&u_code=ejaikd8elj8058&preview_pb=0&sharer_language=en&_d=ejaij098emc1h5&share_item_id=7592315088418229524&source=h5_m&timestamp=1767796279&user_id=7483197776647635989&sec_user_id=MS4wLjABAAAAN7fVbcc0mzRzgIxdVwTekj-Bzgfq381B8aILPWs15fqP6aFNZ5GwIpbLEwMTYvVW&item_author_type=2&social_share_type=0&utm_source=copy&utm_campaign=client_share&utm_medium=android&share_iid=7568740291232040721&share_link_id=3704f903-f8e3-4f92-8cbe-059cd3640d9e&share_app_id=1233&ugbiz_name=MAIN&ug_btm=b8727%2Cb2878&link_r...
Wani na Kusa da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari yayi magana kan Malamin da aka ce yana son auren Hajiya A’isha Buhari

Wani na Kusa da tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari yayi magana kan Malamin da aka ce yana son auren Hajiya A’isha Buhari

Duk Labarai
Bashir Ahmad yayi magana kan jita-jitar auren Shiekh Pantami da Aisha Buhari Wannan ba labari ba ne da ya kamata ma a tsaya ana ƙoƙarin ƙaryata shi, domin duk wani mai hankali ba zai ɗauke shi da muhimmanci ba. Sai dai tunda har yanzu wasu na ci gaba da yaɗa wannan jita jitar, ya zama dole a fayyace gaskiya. Labarin da wasu ke yadawa cewa Hajiya Aisha Buhari ta amince za ta auri Sheikh Isa Ali Pantami ƙarya ce tsagwaronta. Babu ko ƙwayar gaskiya a cikinsa kwata-kwata. -inji Bashir Ahmad tsohon hadimin margayi Buhari Me zaku ce? Daga Kafar Ayau News
Kalli Bidiyon: Gwamna Abba ya bayyana wata Magana da Kwankwaso yayi da bai ji dadinta ba

Kalli Bidiyon: Gwamna Abba ya bayyana wata Magana da Kwankwaso yayi da bai ji dadinta ba

Duk Labarai
An ga wani tsohon Bidiyon gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf ya na fadar wata magana da Kwankwaso yayi wadda bai ji dadinta ba. Bidiyon dai tsohone amma yana ta yawo a kafafen sada zumunta. An ji Abba yana cewa, Kwankwaso yace idan sun nemi shawara zai basu idan basu nema ba zai zuba musu ido. Saidai Abban yace bai ji dadin wannan magana ba dan har sai da ya je ya samu Kwankwaso akan maganar. https://twitter.com/i/status/2008838947787731344
‘Yan Najeriya sun biya Naira Tiriliyan 1.13 a matsayin kudin wutar Lantarki a watanni 6 da suka gabatà

‘Yan Najeriya sun biya Naira Tiriliyan 1.13 a matsayin kudin wutar Lantarki a watanni 6 da suka gabatà

Duk Labarai
Rahotanni daga hukumar kula da wutar Lantarki ta kasa,NERC sun bayyana cewa, 'yan Najeriya sun biya jimullar Naira Tiriliyan 1.13 a matsayin kudin wutar a cikin watanni 6 da suka gabata. Hakan na zuwane duk da kukan rashin wutar da 'yan Najeriyar ke yi. A shekarar data gabata dai Wutar Lantarkin Najeriya ta samu tangarda sosai. Kuma Gwamnatin ta bayyana cewa kudin tallafin wutar da take bayarwa sun haura Tiriliyan 2.