Amfanin kanunfari ga budurwa
Kanumfari yana da matukar Amfani ga Budurwa dama sauran mata gaba daya.
Da farko dai ana amfani da Kanunfari wajan magance matsalar ciwon mara da sauran ciwukan da ake ji a lokacin Al'adar mata.
Hakanan Kanunfari yana kuma taimakawa sosai wajan magance matsalar ciwon daji na mama, watau Breast cancer da mata ke fama dashi.
Hakanan Kanunfari yana maganin kurajen fuska sosai. Yana kuma hana tattarewar fata yanda fata zata zama kamar ta matashiya.
Hakanan Mata na iya amfani da Kanunfari wajan karawa kansu ni'ima da kuma samun gamsuwa yayin jima'i.
Yanda mata zasu hada Kanumfari dan amfaninsu:
Dan Magance matsalar ciwon mara da sauransu lokacin al'ada, mata na iya hada shayin Kanunfari a rika sha kadan-kadan.
Hakanan dan magance matsalar kurajen fuska ko magance matsalar t...