Monday, December 15
Shadow
Ku hadani da Yahya Haifan, Naji yana cika bakin a cikin mintuna 5 zai iya kare Malam Lawal Triumph>>Inji Malama Jamila Abubakar

Ku hadani da Yahya Haifan, Naji yana cika bakin a cikin mintuna 5 zai iya kare Malam Lawal Triumph>>Inji Malama Jamila Abubakar

Duk Labarai
Malama Jamila Abubakar ta nemi a hadata da Malam Yahya Haifan su yi maqabala. Malama ta bayyana hakane inda take tuhumar Haifan kan cewa a cikin mintuna 5 zai warware zargin da akewa Malam Lawal Triumph. Malama Jamila ta zargi 'yan Izala da Ta'addanci. Kalli Bidiyon jawabinta anan https://vt.tiktok.com/ZSDK5XaTt
Soke Faretin Sojoji na ranar ‘yanci ya bani damar yin bacci da cin abincin safe da kyau>>Inji Shugaba Tinubu

Soke Faretin Sojoji na ranar ‘yanci ya bani damar yin bacci da cin abincin safe da kyau>>Inji Shugaba Tinubu

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, soke faretin sojoji na ranar 'yanci ya bashi damar yin bacci da kyau da kuma in abincin safe da kyau. Shugaban ya bayyana hakane yayin bude wani dakin kimiyyar zane-zane da aka sakawa sunan Wole Soyinka. Fadar Shugaban kasa tun kamin ranar 'yanci ta sanar da cewa, babu faretin sojoji da aka saba yi.
DJ ya dakatar da kida bayan da aka hanashi Abinci a wajan taro

DJ ya dakatar da kida bayan da aka hanashi Abinci a wajan taro

Duk Labarai
Wani DJ me saka kida, ya dakatar da kida a wajan bikin da ya je bayan da aka hanashi abinci yayin da ake ta baiwa sauran mutanen abinci. DJ din ya dakatar da kidan sannan ya kashe Janareta dan ya nuna fushinsa. A wani Bidiyonsa da ya watsu a kafafen sada zumunta, an ga DJ din yana kumfar baki da fadin cewa, ba'a masa adalci ba. Saidai daga baya an bashi baki inda aka masa alkawarin samar masa da abinci da zai ci.
Maza sun yi karanci dole mata su hakura a rika auren 4>>Inji Tauraruwar fina-finan Kudu, Bimbo Akintola

Maza sun yi karanci dole mata su hakura a rika auren 4>>Inji Tauraruwar fina-finan Kudu, Bimbo Akintola

Duk Labarai
Tauraruwar fina-finan Kudu, Bimbo Akintola ta bayyana cewa, maza sun yi karanci dan haka dolene mata su hakura a rika yin auren mata 4. Tace hakan ne zai kawo saukin dadewar mata da suke yi a gidajen iyayensu ba tare da aure ba. Ta bayyana cewa, bayan haka ma auren mace fiye da daya al'adar Yarbawa ce dan haka ya kamata a ci gaba da dabbaka wannan al'ada.
Gwajin kwayoyin Halitta na DNA dan a gano cewa dan da aka haifa dan miji ne ko dan Zyna ne Haramun ne a musulunci>>Inji Malam Dr. Sharafdeen Gbadebo

Gwajin kwayoyin Halitta na DNA dan a gano cewa dan da aka haifa dan miji ne ko dan Zyna ne Haramun ne a musulunci>>Inji Malam Dr. Sharafdeen Gbadebo

Duk Labarai
Malamin Addinin Musulunci, Dr. Sharafdeen Gbadebo wanda yayi wa'azi da yarbanci ya bayyana cewa, yin Gwajin kwayoyin halitta na DNA haramun ne a Musulunci. Ana yin gwajin DNA ne dan gano da na wanene musamman idan aka samu gaddama tsakanin mata da miji, mijij yana zarginta da kawo mai dan da ba nashi ba. Malamin yace a addini babu tsarin yin gwajin DNA. Yace abinda addini ya zo dashi, rantsuwa ake yi tsakanin matar da mijin.
Kalli Bidiyo: Itama Momi Gombe ta mallaki sabuwar Wayar iPhone 17 pro max ta Miliyoyin Naira

Kalli Bidiyo: Itama Momi Gombe ta mallaki sabuwar Wayar iPhone 17 pro max ta Miliyoyin Naira

Duk Labarai
Rahotanni sun ce Tauraruwar fina-finan Hausa, Momi Gombe ta mallaki Sabuwar Wayar iPhone 17 pro max ta Miliyoyin Naira. An ga Momi tana nuna sabuwar wayar tata inda ake mata kirari. A baya dai Ummi Gayu da Asiya Chairlady ne suka bayyana mallakar wayar a Kannywood. https://www.tiktok.com/@haseenamakeup/video/7556239686914608392?_t=ZS-90CvbYzp2wr&_r=1