Alamun ciki a watan farko
Watakila kinga canji a jikinki kin fara tambayar me ya faru? Ko kuma watakila batan wata ko daukewar jinin al'adane kadai kika fuskanta.
Wasu matan na ganin alamun shigar ciki a watan Farko yayin da wasu basa gani.
Ga alamun da ake gani na shigar ciki a watan Farko:
Rashin zuwa jinin Al'ada ko batan wata: Musamman idan kina ganin jinin al'adarki akai-akai amma baki ganshi ba wannan karin, zai iya zama kina da ciki.
Canjawar Dabi'a: Zai zamana kina saurin fushi ko kuma haka kawai ki rika jin bacin rai, hakanan zai iya zama kina dariya akan abinda bai kai ayi dariya akansa ba.
Cikinki zai rika kuka ko kuma kiji kamar kinci abinci: Cin abinci irin su Aya, Tuwon masara, dawa, ko gero wanda ba'a barza ba, Kwakwa, wake zasu taimaka miki magance wannan matsalar.
Zaki ji gabobink...