Kungiyar Hezbollah ta ki amincewa da sulhu da kasar Israela
Kungiyar Hezbollah ta ki amincewa da tayin yin Sulhu da kasar Israela.
Shugaban Hezbollah din, Hassan Nasrallah ne ya bayyana haka.
Fada na ci gaba da kazancewa tsakanin kasar Israela da Hezbollah.
Ko da a jiya sai da Hezbollah tawa kasar Israela ruwan bamabamai masu yawa.
Kungiyar dai ta Hezbollah ta bayyana cewa tana goyon bayan samun 'yancin Falasdinawa.