Wasu na shirin gudanar da zanga-zangar lalata Ranar Dimokuraɗiyya – DSS
Rundunar 'yansadan Najeriya ta farin kaya a Najeriya (DSS) ta ce ta samu labarin wasu na shirin fakewa da gudanar da zanga-zanga a faɗin ƙasar da zimmar aikata laifuka kuma ta nemi 'yan ƙasa su guji yin hakan.
Wata sanarwa da rundunar ta fitar ta ce an shirya zanga-zangar ne da gangan "domin ta dace da Ranar Dimokuraɗiyya ta 12 ga watan Yuni".
Ta alaƙanta zanga-zangar da gwagwarmayar neman ƙarin albashi mafi ƙaranci da ƙungiyoyin ƙwadago ke yi, inda ta ce "gwamnatin tarayya ta fi son a warware matsalar cikin lumana har ma da maganar mafi ƙarancin albashi".
"Sai dai kuma DSS na jaddada aniyarta ta kare ƙasar daga duk wani yunƙuri na wasu ƙungiyoyi na karya doka da oda. Sannan kuma za ta hada kai da sauran jami'an tsaro don kare rayuka da dukiyoyi," in ji sanarwar.
Ita ma runduna...