Kalli Hotunan wata maboyar ‘yan Bin-di-ga da ‘yansanda suka gano
'Yansanda a Abuja sun bankado wata maboyar 'yan Bindiga dake gidan Dogo a cikin daji Kweti dake kusa da babban birnin tarayya, Abuja.
Kakakin 'yansandan Abuja, SP Josephine Adeh ta bayyana hakan ga manema labarai inda tace an bankado maboyar ne bayan samun bayanan sirri.
An kama mutane 4 da ake zargi bayan da aka yi musayar wuta tsakaninsu da jami'an tsaron.
Dukansu sun amsa cewa su masu garkuwa da mutanene.
An kubutar da wasu da suka yi garkuwa dasu inda aka mika su hannun 'yan uwansu.