Saturday, December 13
Shadow
Kalli Bidiyon: Wannan shekarar mun yi Maulidi me tsafta, Ba’a ce an rika ganin Shehu a Sama ko a jikin gini ba, ganin cewa kawai muka rika yi yana wucewa ta gaban mu>>Inji Anisee

Kalli Bidiyon: Wannan shekarar mun yi Maulidi me tsafta, Ba’a ce an rika ganin Shehu a Sama ko a jikin gini ba, ganin cewa kawai muka rika yi yana wucewa ta gaban mu>>Inji Anisee

Duk Labarai
Shahararren dan Darika, Alhaji Anisee Ya bayyana cewa a bana sun yi Maulidi me tsafta. Ya bayyana cewa basu rika ganin Shehu a Gajimare ba ko kuma a jikin gine-gineba, Yace a wannan shekarar sun rika ganin Shehu ne a zahiri yana wucewa ta gabansu. https://www.tiktok.com/@alhajianisee1/video/7547230384145173768?_t=ZS-8zYJAL0uyAL&_r=1
Kalli Bidiyon: Yanda Farfesa Sheikh Isa Ali Pantami ya fashe da kuka saboda takaicin masu son raba kan Hausawa da Fulani

Kalli Bidiyon: Yanda Farfesa Sheikh Isa Ali Pantami ya fashe da kuka saboda takaicin masu son raba kan Hausawa da Fulani

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama, Sheikh Isa Ali Pantami ya nuna damuwa matuka akan masu son kawo rabuwar kai tsakanin Hausawa da Fulani. A wani wa'azinsa, An ga Malam ya fashe da kuka inda yace yanzu har akwai wanda zai kawo mana kabilanci kuma har a yadda dashi? https://www.tiktok.com/@professorisaalipantami/video/7545900646709595410?_t=ZS-8zYC14zKUIz&_r=1
Kalli Bidiyo: Yanda wasu musulmai a kasar Amurka suka fito suna neman a Haramta Shan giya, Cin Nqmqn Alade da Caca

Kalli Bidiyo: Yanda wasu musulmai a kasar Amurka suka fito suna neman a Haramta Shan giya, Cin Nqmqn Alade da Caca

Duk Labarai
Wannan wasu musulmai ne a kasar Amurka da suka fito suke zanga-zanga dan neman a haramta cin naman Alade da shan giya da caca Lamarin ya farune a Texas inda abin ya matukar dauki hankula sosai wasu na cewa suna da 'yancin yin hakan wasu kuma na ganin yin hakan ganganci ne. Kalli Bidiyonsu a kasa: https://twitter.com/RadioGenoa/status/1964713441899565330?t=xzY6NH0Q3Rz5MgL3aZbY4A&s=19
Kalli Bidiyon: Ana ta cece-kuce, ‘Yan Najeriya na mamaki bayan ganin katafaren gidan tsohon Gwamnan Abia, Orji Kalu a kasar Amurka

Kalli Bidiyon: Ana ta cece-kuce, ‘Yan Najeriya na mamaki bayan ganin katafaren gidan tsohon Gwamnan Abia, Orji Kalu a kasar Amurka

Duk Labarai
An ga katafaren gida na Alfarma da tsohon gwamnan jihar Abia, Orji Kalu ya mallaka a Maryland dake kasar Amurka. Lamarin ya dauki hankula sosai inda akai ta cece-kuce wasu na fadin cewa abin birgewane inda wasu kuma ke cewa ba da kudinsa ya saya ba. https://twitter.com/ChuksEricE/status/1964690041445503097?t=QNJuC22yYEtxJ5F_MOYxzQ&s=19
Baiwa jami’an mu kudi, cin hanci laifi ne, ku daina dauke musu hankali daga gudanar da aiki yanda ya kamata>>Hukumar ‘Yansandan Najeriya ta gargadi mutane

Baiwa jami’an mu kudi, cin hanci laifi ne, ku daina dauke musu hankali daga gudanar da aiki yanda ya kamata>>Hukumar ‘Yansandan Najeriya ta gargadi mutane

Duk Labarai
Hukumar 'yansandan Najeriya ta garagadi Mutane da cewa, baiwa 'yansandan Najeriya kudi ko cin hanci a yayin da suke bakin aiki shima laifi ne. Hukumar ta gargadi 'yan Najeriya da su yi hankali su daina daukewa 'yansandan hankali daga aikin da suke. Sanarwar ta fito ne daga bakin hukumar 'yansandan babban birnin tarayya Abuja. https://twitter.com/FCT_PoliceNG/status/1964752773083181153?t=Hw13v97hldjZVynO-RQ3Lg&s=19
Gwamnati ta shiga tsakani a rikicin Dangote da ‘yan kasuwar man fetur da suke zargin Dangoten da yin kaka gida a harkar man fetur

Gwamnati ta shiga tsakani a rikicin Dangote da ‘yan kasuwar man fetur da suke zargin Dangoten da yin kaka gida a harkar man fetur

Duk Labarai
Ministan Kwadago, Muhammadu Dingyadi ya kira Kungiyar ma'aikatan man fetur ta kasa, NUPENG da kuma kamfanin matatar man Dangote dan ya zauna dasu kan rikicin da ya bulla a tsakaninsu. Kungiyar ta NUPENG ta zargi Dangote da yin kaka gida a harkar man fetur da rashin biyan ma'aikata da kyau da rashin baiwa ma'aikata damar shiga kungiyoyin fafutuka na ma'aikata da sauransu. Kungiyar Tuni ta shirya shiga yajin aiki dan nuna rashin amincewa da tsare-tsaren Matatar mam fetur ta Dangote wanda tace ya sabawa ka'idar aiki wanda kuma tuni Kungiyar Kwadago ta NLC ta amince da wannan yajin aiki. Saidai wannan kira da ministan ya musu ana sa ran dai kawo karshen lamarin.
Kalli Bidiyo: Kafurci da Munafurci ne kesa ake cewa ana tsananin matsalar tsàrò a Najeriya>>Inji Sheikh Sani Yahya Jingir

Kalli Bidiyo: Kafurci da Munafurci ne kesa ake cewa ana tsananin matsalar tsàrò a Najeriya>>Inji Sheikh Sani Yahya Jingir

Duk Labarai
Babban malamin addinin Islama, Sheikh Sani Yahya Jingir ya bayyana cewa, Kafurci da Munafurci ne ke sa mutane cewa ana tsanin matsalar tsaro a Najeriya. Malam ya bayyana hakane a yayin da yake wa'azi inda yace su dai sun je jihar Kebbi sun dawo Lafiya. Kalli Bidiyon jawabinsa: https://www.tiktok.com/@i_am_saeed01/video/7546550346475179270?_t=ZS-8zXbRcRPa4W&_r=1
Abin takaici ne ace Kungiyar mu ta Izala taje jihar Kebbi an yi wa’azi amma ba’a tabo maganar tsaron yankin ba a wajan wa’azin>>Inji Sheikh Yusuf Sambo Rigachukun

Abin takaici ne ace Kungiyar mu ta Izala taje jihar Kebbi an yi wa’azi amma ba’a tabo maganar tsaron yankin ba a wajan wa’azin>>Inji Sheikh Yusuf Sambo Rigachukun

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama, Sheikh Yusuf Sambo Rigachukun ya bayyana rashin jin dadinsa game da wa'azin Izala da aka yi a jihar Kebbi amma ba'a yi maganar matsalar tsaron yankin ba. Malam yace mutane sun fi 100 da suka kirashi suna nuna damuwa akan Lamarin. Malam yace kuma an yi hakane wai dan kada a batawa Gwamnati rai. Yace suma suna tare da wasu jami'an Gwamnatin amma hakan ba zai hanasu fadar gaskiya ba. https://www.tiktok.com/@abdullahingwandutv/video/7545975485742763284?_t=ZS-8zXZs1JmLPV&_r=1
Ance Maulidin Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ake yi to me ya kawo hoton Sheikh Inyas a rigunan masu maulidin, sannan Mun fito zamu shago an rufe mana hanya, me yasa ba za’a iya yin Maulidin a gida ba sai an rufewa mutane hanya? Rukayya ta tambaya

Wannan me yin Tiktok din me suna Rukayya tace tambayarta shine an ce Maulidin Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ake yi amma kuma gashi sai kaga hotunan Inyas a jikin masu Maulidi me yasa haka? Sannan ta yi tambayar cewa, me yasa ba za'a yi Maulidi a gida ba sai an tare hanya saboda ta fito zata je shago amma aka tare musu hanya. Sannan tace me yasa Shehunan Darika ke yafa koren mayafi? https://www.tiktok.com/@rukaiya_magaji/video/7547348972520754439?_t=ZS-8zXYmWviWDw&_r=1