Monday, December 15
Shadow
Allah Sarki: Kalli Bidiyon yanda Saheer Abdul ya fashe da kuka saboda irin mata ke aika masa ya taya su addu’ar neman mijin aure da kuma neman zaman lafiya da mazajensu

Allah Sarki: Kalli Bidiyon yanda Saheer Abdul ya fashe da kuka saboda irin mata ke aika masa ya taya su addu’ar neman mijin aure da kuma neman zaman lafiya da mazajensu

Duk Labarai
Tauraron fina-finan Hausa, Saheer Abdul da ya je Madina, ibada da sayar da garin Danwake yace da yawan wadanda ke aika masa da neman ya taya su da addu'a matane. Yace kuma yawanci suna cewa ne ya nema musu addu'ar Allah ya basu mazajen aure wasu kuma suna kiran ya taya su da addu'ar Allah yasa su samu zaman lafiya da mazansu. Yace irin labaran da matan ke bashi akwai ban tausai. Ya sha Alwashin taya su da addu'a. https://www.tiktok.com/@mr_saheeer/video/7548756716633066760?_t=ZS-8zeyAXIqm5w&_r=1
Ji Labarin yanda aka yaudari wata matashiyar Najeriya aka kaita kasar Mali da sunan zata yi aiki a Supermarket amma aka ce Qaruwanciy zata yi

Ji Labarin yanda aka yaudari wata matashiyar Najeriya aka kaita kasar Mali da sunan zata yi aiki a Supermarket amma aka ce Qaruwanciy zata yi

Duk Labarai
Wata matashiyar Najeriya me suna Faith Joseph ta ki amincewa da yin karuwanci bayan da aka yaudareta aka kaita kasar Mali da sunan zata yi aiki a Supermarket. Matashiyar na aikin gida ne a Afuze, Owan East dake jihar Edo inda aka ce za'a kaita Legas dan ta yi aiki a Supermarket. Saidai daga baya an tafi da ita kasar Mali, tace sina zuwa aka kaita wajan wata mata wadda Magajiyace, watau uwar Karuwai, data lura da haka sai tace bata yadda ba, ba zata yi ba. Saidai magajiyar ta gaya mata cewa, aikuwa saidai idan an kawo wata da zata maye gurbinta ne sannan zata iya komawa gida Najeriya. Matashiya, Faith haka ta zauna har Allah yasa ta lura da wani Ofishin 'yansanda inda ta tsere zuwa can. Daga baya dai ta samu an dawo da ita zuwa gida Najeriya. Shugaban hukumar kula da 'y...
Da Duminsa: An samu Matuka jirgin saman Air Peace da shaye-shayen abubuwan Maaye

Da Duminsa: An samu Matuka jirgin saman Air Peace da shaye-shayen abubuwan Maaye

Duk Labarai
Rahotanni daga hukumar bincike ta kasa, The Nigerian Safety Investigation Bureau sun bayyana cewa, an samu biyu daga cikin matuka jirgin saman kamfanin Air Peace da shaye-shayen miyagun kwayoyi. Abubuwan da aka samesu da sha shine kwayoyi da kuma giya. Hakan na zuwane bayan da jirgin da suke tukawa ya kaucewa hanya a filin jirgin samana na Fatakwal a ranar July 13, 2025. Me magana da yawun hukumar binciken ta Najeriya, Mrs Bimbo Olawumi Oladeji ce ta tabbatar da hakan ga manema labarai na jaridar Punchng. An gano cewa matuka jirgin sun yi wasa da rayuwar mutane 103 da suke dauke dasu a wancan lokacin.
Jihar Delta ta yi dokar hana Ma’aikatan jihar Tara gemu da yawa

Jihar Delta ta yi dokar hana Ma’aikatan jihar Tara gemu da yawa

Duk Labarai
Jihar Delta ta yi sabuwar doka game da irin kayan da ya kamata ma'aikatan jihar maza da mata su rika sakawa. A wata sanarwa data fitar a yau, Alhamis, Jihar tace dolene ma'aikata su rika saka kayan mutunci a yayin da suka je wajan aiki. Sanarwar tace ana tsammanin maza su rika saka kwat ko riga 'yar ciki su tsuke in banda ranar Juma'a da zasu iya saka kayan gida. Hakanan ba'a so mutum ya tara gemu da yawa ba aski, ba gyara. Mata kuma su saka siket wanda zai rika wuce gwiwarsu.
Da Duminsa: Gwamnatin tarayya ta soke harajin kaso 5 na kamfanonin Sadarwa wanda yasa kudin data dana kira suka kara tsada

Da Duminsa: Gwamnatin tarayya ta soke harajin kaso 5 na kamfanonin Sadarwa wanda yasa kudin data dana kira suka kara tsada

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, Gwamnatin tarayya ta soke harajin Kaso 5 cikin 100 na kamfanonin sadarwa wanda yasa kudin data dana kiran waya suka kara tsada. Hakan na zuwane daga bakin shugaban hukumar sadarwa ta kasa, NCC, Dr. Aminu Maida inda yace shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ne ya bayar da umarnin a yi hakan. Yace shugaban ya yi hakan ne dan saukakawa 'yan Najeriya da suka fuskanci tsadar kudin kira dana data. Harajin dai tun bayan kaddamar dashi aka kara kudin kira dana data da kaso 50 cikin 100. Hakanan jaridar Punchng tace tun a lokacin mulkin Buhari ne aka gabatar da wannan haraji wanda ya samu suka daga kamfanonin sadarwa da masu amfani da wayoyi.
Kalli Bidiyo: Da na gama aiki a matsayin Minista an yi ta fama dani in rike motocin da Gwamnati ta bani ina aiki dasu amma naki na mayarwa da gwamnati kayanta>>Inji Farfesa Sheikh Isa Ali Pantami

Kalli Bidiyo: Da na gama aiki a matsayin Minista an yi ta fama dani in rike motocin da Gwamnati ta bani ina aiki dasu amma naki na mayarwa da gwamnati kayanta>>Inji Farfesa Sheikh Isa Ali Pantami

Duk Labarai
Babban Malamin Addinin Islama, Farfesa Sheikh Isa Ali Pantami ya bayyana cewa, da ya kammala aikin gwamnati a watan Mayu na shekarar 2023 ya tattara motocin gwamnati 6 da aka basu yana aiki dasu ya mayarwa da gwamnati kayanta. Malam yace akwai wani abokinsa da ya gaya mai cewa ba'a mayarwa rikewa ake haka aka saba, saidai malam yace ya nuna masa inda yake rubuce a doka. Yace indai ba doka bace ta zo dashi a rubuce dan haka shi yana ganin wannan motoci ba halas dinsa bane dan haka ya mayar dasu. https://www.tiktok.com/@sheihk.prof.panta/video/7547065656139730197?_t=ZS-8zdvu7lHrsX&_r=1 Malam ya bayyana hakane a yayin karatu da yake gabatarwa.
Kalli Bidiyon: Sati daya da Bashi Miliyan 20, Mutane sun yi mamakin ganin Bidiyon malam Nata’ala inda da yawa ke cewa ya warke

Kalli Bidiyon: Sati daya da Bashi Miliyan 20, Mutane sun yi mamakin ganin Bidiyon malam Nata’ala inda da yawa ke cewa ya warke

Duk Labarai
Sabon Bidiyon Malam Nata'ala bayan da Shugaban kasar Nijar ya bashi sama da Naira Miliyan 20 dan yayi magani ya baiwa mutane mamaki. An ga malam Nata'ala har yayi kiba inda mutane ke cewa, ya warke. Hakan na zuwane kwanaki kadan bayan da Malam Nata'ala ya roki a tallafa mai da kudi dan yayi aikin cutar daji data kamashi. https://www.tiktok.com/@aabdallahfatgmail.com1/video/7547782055367609606?_t=ZS-8zdWOub9yfR&_r=1