Kanfanonin dake hako danyen man fetur a Najeriya sun ki sayar min dashi, sun kwammace su kaishi kasashen waje>>Dangote
Babban Attajirin Afrika, Aliko Dangote ya bayyana cewa, kamfanonin dake hako man fetur a Najeriya basa son sayar masa da danyen man fetur din.
Ya bayyana hakane a hirar da gidan talabijin na CNN suka yi dashi inda yace kamfanonin sun saba da kai man fetur kasashen waje suna samun kudi dan haka sun ki sayar masa da danyen man.
Yace da za'a sayar masa da danyen man, babu bukatar a rika sayo tataccen man daga kasashen turawa.
Yace amma 'yan kasuwa dake shigo da man fetur din daga kasashen waje basa son hakan dan kuwa zasu rasa aiki.
Saidai gwamnatin Najeriya ta bakin hukumar dake kula da harkar man fetur din, NUPRC, ta bayyana cewa zasu shiga tsakanin Dangote da kamfanonin dake hako man fetur din.
Wakilin hukumar, Olaide Shonola ne ya bayyana haka a hirar da jaridar Punch ta yi...