Zan samu ribar Dala Biliyan $30 a karshen shekarar 2024>>Dangote
Attajirin Najeriya, Aliko Dangote ya bayyana cewa nan da karshen shekarar 2024 zai samu ribar zunzurutun kudi har Dala Biliyan $30.
Dangote ya bayyana hakane a hirar da CNN ta yi dashi.
Ya bayyana cewa, hakan zai sa kamfaninsa ya shiga sanun kamfanoni 120 mafiya karfi a Duniya.
Dangote dai a yanzu yana da mamatar man fetur wadda take daya daga cikin matatun man da ke da girma a Duniya.