‘Tattalin arziƙin Najeriya na bunƙasa’
Ministan Kuɗi na Najeriya, Wale Edun, ya bayyana cewa tattalin arzƙin ƙasar na farfaɗowa, wanda hakan zai sa nan da ƴan watanni a daina samun hauhawar farashin kayayyaki da ke addabar jama'a.
Mista Edun ya faɗi hakan ne a yayin wata hira da tashar talabijin ta Channels ta yi da shi, jiya Lahadi.
A rahotonta na watan Afirilu, kan farashin kayayyaki, Hukumar Ƙididdiga ta ƙasar (National Bureau of Statistics) ta nuna cewa hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya ta ƙaru zuwa kashi 33.20 cikin ɗari a watan Maris na wannan shekara — tashin ya ƙaru daga kashi 31.70 cikin ɗari a watan Fabarairu.
Hukumar ta ce tashin farashin kayan abinci ya ƙaru da kashi 40.01 cikin ɗari a cikin watan na Afirilu.
Duk da waɗannan alƙaluma da hukumar ta fitar, Ministan ya ce tattalin arzƙin Najeriyar na k...