Monday, December 15
Shadow
Kalli Bidiyo: Abinda ‘Yan Darika suke yi, yafi wanda Marigayi Dan Damusa Yake yi na aika mutane lahira ba gaira ba dalili>Inji Dr. Hussain

Kalli Bidiyo: Abinda ‘Yan Darika suke yi, yafi wanda Marigayi Dan Damusa Yake yi na aika mutane lahira ba gaira ba dalili>Inji Dr. Hussain

Duk Labarai
Malami me wa'azi a Tiktok, Dr. Hussain ya bayyana cewa, abinda wasu 'yan darija suke yi na "Shirka" yafi abinda dan daba, Habu Dan Damisa da aka kashe a Kaduna na kisan mutane ba gaira babu dalili. Malamin ace karkari dai ace habu yayi shaye-shaye ko kisa da sauransu, yace to hakan bai kai shirka ba a wajan Allah. Sannan malamin yace Dabbaci da jahilci ne murna da mutuwar Dan Damisa, Addu'a ya kamata a yi masa. https://www.tiktok.com/@dr.hussainkano5/video/7544116373421690168?_t=ZS-8zKrppT3L0a&_r=1
Kalli Bidiyo: Na shirya zuwa Saudiyya dan in Tsynewa Azzalumai, Inji tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai bayan watsa taronsu na ADC a Kaduna

Kalli Bidiyo: Na shirya zuwa Saudiyya dan in Tsynewa Azzalumai, Inji tsohon Gwamnan Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai bayan watsa taronsu na ADC a Kaduna

Duk Labarai
Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya bayyana cewa, ya shirya zuwa Kasa me tsarki dan tsinewa Azzalumai. Ya bayyana hakane a Bidiyon jawabinsa biyo bayan harin da 'yan daba suka kai suka tarwatsa taronsu na jam'iyyar ADC ranar Asabar. El-Rufai ya bayyana cewa, ya tsinewa wadanda suka aikata wannan abu. https://www.tiktok.com/@mohammed.adamu69/video/7544467195057786130?_t=ZS-8zKqoveRqTZ&_r=1
Kalli Bidiyon: Hotunan da aka rika yadawa ina daukar hoto, tsaffin hotunane>>Gwamna Dikko Radda

Kalli Bidiyon: Hotunan da aka rika yadawa ina daukar hoto, tsaffin hotunane>>Gwamna Dikko Radda

Duk Labarai
Gwamnan jihar Katsina, Umar Dikko Radda ya bayyana cewa, Hotunan da aka rika yadawa inda aka ganshi yana daukar hoto a kasashen Turawa tsaffin hotunane. Ya bayyana hakane a wata hira da aka yi dashi. !A lokacin da aka kai hari wani kauyen Mantau dake Malunfashi jihar Katsina inda aka kashe masallata da yawa, an rika yada hotunan inda aka rika cewa, Gwamna na can kasashen Turai yana hutawa yayin da aka kashe mutane a jihar Katsina. Gwamna Dikko Radda yace neman lafiya yaje, kuma yace a wancan lokacin shi ba gwamnan jihar Katsina bane, sabida ya mika ragamar mulki a hannun mataimakinsa.
Kalli Bidiyon yanda Matasa marasa jin magana suka tashi taron jam’iyyar ADC da aka yi a Kaduna wanda El-Rufai ya jagoranta, Matasan sun yi hakan ne a gaban ‘yansanda inda a cikin Bidiyon ake jin mutane na cewa menene Amfanin ‘yansandan?

A jiya ne dai rahotanni suka bayyana cewa, An kaiwa taron jam'iyyar ADC hari a Kaduna inda aka lalata dukiyoyi. Taron wanda tsohon gwamnan jihar, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya jagoranta ya dauki hankula sosai. Daga baya, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai ya fito inda yake bayyana zargin Gwamnan jihar Kaduna, Malam Uba Sani da daukar nauyin wadanan 'yan daban. https://www.tiktok.com/@saiduturakikd/video/7544443730007297301?_t=ZS-8zKfdtPSAaW&_r=1 https://www.tiktok.com/@saiduturakikd/video/7544443928754294037?_t=ZS-8zKfgQsbAG1&_r=1
Kalli Bidiyo: Duk wanda baya Maulidi ba Musulmi bane>>Inji Sheikh Maqari

Kalli Bidiyo: Duk wanda baya Maulidi ba Musulmi bane>>Inji Sheikh Maqari

Duk Labarai
Malamin Addinin Islama, Sheikh Ibrahim Maqari ya bayyana cewa, duk wanda baya maulidin Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) ba musulmi bane. Ya bayyana cewa, Maulidi yana nufin murna da zuwan Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) Duniya, amma yanda mutum ya zabi yayi wannan murnar ne ya banbanta. https://www.tiktok.com/@jeapeey/video/7543227086580862215?_t=ZS-8zJP26muF5V&_r=1
Kalli Bidiyo: Tsohuwar jarumar fina-finan Hausa, Farida Jalal ta zama Sayyada me waken yabon Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam), Tace hakan ya fi a kirata da Kàrùwà

Kalli Bidiyo: Tsohuwar jarumar fina-finan Hausa, Farida Jalal ta zama Sayyada me waken yabon Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam), Tace hakan ya fi a kirata da Kàrùwà

Duk Labarai
Tsohuwar Tauraruwar fina-finan Hausa, Farida Jalal ta bayyana cewa, ta koma yabon Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam) An ga Farida tana waken yabon Annabi saidai wani yace mata haka tsaffib 'yan matan Kannywood suke karewa, saidai ta mayar masa da martanin cewa yafi a kirata da Karuwa. https://www.tiktok.com/@shairanannabi2/video/7541086338641038597?_t=ZS-8zJK0S8J9If&_r=1 https://www.tiktok.com/@teemahcool0/video/7544019346889346325?_t=ZS-8zJLIKZFofZ&_r=1
Da Duminsa: Wike ya bayyana cewa ranar 18 ga watan September Gwamnan Jihar Rivers, Simi Fubara da majalisar jihar zasu koma bakin aiki

Da Duminsa: Wike ya bayyana cewa ranar 18 ga watan September Gwamnan Jihar Rivers, Simi Fubara da majalisar jihar zasu koma bakin aiki

Duk Labarai
Ministan babban birnin tarayya Abuja, Nyesom Wike ya bayyana cewa, nan da ranar 18 ga watan Satumba Gwamnan jihar Rivers, Simi Fubara zai koma bakin aikinsa tare da 'yan majalisar jihar. Wike ya bayyana hakane bayan ya kada kuri'ar sa a zaben kananan hukumomi da ake a jihar ta Rivers Ranar Asabar. Wike ya kada kuri'ar sa a rumfar zabe me lamba 7 a mazabar ,ward 9 dake yankin Rumuepirikom na karamar hukumar Obio-Akpor. Wike yace an yi zaben lami lafiya. Yace nan da ranar 18 ga watan Satumba mulkin karta kwana zai kare kuma Gwamnan jihar Simi Fubara da 'yan majalisar jihar zasu dawo bakin aiki
Mun warware matsalolin aure aƙalla 600 a shekara ɗaya – HISBAH

Mun warware matsalolin aure aƙalla 600 a shekara ɗaya – HISBAH

Duk Labarai
A jihar Kano, hukumar Hisba ta sanar da cewa ta warware korafe-korafe ko rigingimu tsakanin ma’aurata har dari shida da ashirin da daya cikin shekara daya. Mutuwar aure gagarumar matsala ce da ke shafar mutane, kama daga matan da ake saki da mazan da ‘ya’yan, sanadiyyar wani sabani ko rashin jituwa. Wannan dalili ne yasa hukumar ta HISBA ta ke kokarin sulhunta ma’aurata don su ci gaba da rayuwa cikin fahimtar juna tare da ‘ya’yansu.