A addinance, idan ka ga yarinya, Budurwa kana so, zaka fara zuwa wajan mahaifinta ne ka nemi izini.
Idan kuma ba zaka iya zuwa ba kai tsaye, zaka iya aika magabatanka a nemar maka izini idan ba'a bayar da ita ba.
Idan ka samu aka maka iso to aiki ya ganka.
Anan ne kai kuma aiki ya rage gareka ka samu hanyar da zaka yi nasara soyayyarka ta shiga zuciyarta.
Abubuwan da zaka rika yi dan jan hankalinta:
Ka rika yin kwalliya sosai idan zaka je wajenta.
Ka rika saka turare.
Ka wanke baki.
Ka rika bata labarin abinda bata sani ba.
Ka rika mata kyauta.
Ka rika kokarin sata dariya.
Ka mayar da ita abokiyarka, ka rika neman shawarar ta.
Wannan zai sa ka shiga zuciyarta sosai kuma itama ta ji tana sonka.