Thursday, December 26
Shadow
Zan kori duk ministan da baya aiki yanda ya kamata>>Shugaba Tinubu

Zan kori duk ministan da baya aiki yanda ya kamata>>Shugaba Tinubu

Siyasa
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya bayyana cewa, zai kori duk ministan da baya aiki yanda ya kamata. Tinubu ya bayyana hakane a ganawar da yayi da kungiyar dattawan Arewa ta ACF da yammacin ranar Alhamis. Yace zai ci gaba da yin aiki iya kokarinsa dan ci gaban Najeriya. Ya bayyana cewa, yana godewa 'yan majalisar zartaswarsa kan kokarin da suke amma zai rika dubawa yana tankade da rairaya dan gano wanda basa aiki yanda ya kamata dan canjasu.
Kalli Bidiyo yanda dan majalisar kasar Faransa ya daga tutar Falas-dinawa a yayin zaman majalisar

Kalli Bidiyo yanda dan majalisar kasar Faransa ya daga tutar Falas-dinawa a yayin zaman majalisar

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Dan majalisar kasar Faransa, Sébastien Delogu ya daga tutar Falas-dinawa a farfajiyar majalisar yayin da ake zaman zauren majalisar. Dan majalisar yace kasarsa ta Faransa na da hannu a kisan kare dangin da Israela kewa Falas-dinawa ta hanyar sayarwa da Israelan makamai. Yayi kira ga shugaban kasar, Emmanuel Macron da ya daina sayarwa da Israela makamai. https://twitter.com/sahouraxo/status/1795457671119688144?t=h0iwUNItfTYrx_DDpFfIbA&s=19 Saidai an dakatar dashi sannan aka bashi dakatarwar kwanaki 15. Saidai bayan dakatar dashi, Dan majalisar ya shiga cikin masu zanga-zangar goyon bayan kasar ta Falas-dinawa a kan titi: https://twitter.com/sahouraxo/status/1795788298402557952?t=QXi2U6P3vslbvkahEq1zIA&s=19 Saidai a wani lamari kuma na ban mamaki, shine, kaka...
Kalli Hotuna da bidiyon kisan wulakancin da ‘yan I-POB masu son kafa kasar Biafra sukawa sojojin Najeriya sannan suka kona motar sojojin a jihar Abia

Kalli Hotuna da bidiyon kisan wulakancin da ‘yan I-POB masu son kafa kasar Biafra sukawa sojojin Najeriya sannan suka kona motar sojojin a jihar Abia

Tsaro
Rahotanni sun bayyana cewa, wasu da ake kira da 'yan Bindigar da ba'a sansu ba, watau Unknown Gunmen, amma ana kyautata zaton 'yan kungiyar IPOB ne dake son kafa kasar Biafra sun kashe sojoji 2 a jihar Abia. Sun kashe sojojinne a wani shingen sojojin dake Obikabia jihar ta Abia a ranar tunawa da wadanda suka yi yakin Biafra. A wani bidiyo dake ta yawo a shafukan sada zumunta, an ga 'yan Bindigar bayan sun kashe sojojin suka kuma kona motarsu kurmus. Kalli Bidiyon a kasa: https://twitter.com/MaziEminent/status/1796136640034873771?t=HYb-5JLLECXTz_AC98Phxw&s=19 https://twitter.com/PIDOMNIGERIA/status/1796144862313468210?t=hzr4r1n221O86UTZxEnPQw&s=19 https://twitter.com/Tony_Ogbuagu/status/1796123554682966269?t=rFUU8b3uT0UElDumzNKfSQ&s=19 Tuni dai gwa...
Zamu fitar da matasa miliyan 50 daga Talauci>>Gwamnatin Tarayya

Zamu fitar da matasa miliyan 50 daga Talauci>>Gwamnatin Tarayya

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, zata fitar da matasa miliyan 50 daga Talauci. Ministan kimiyya da fasaha, Chief Uche Geoffrey Nnaji ne ya bayyana haka. Ya bayyana cewa, za'a saka kirkire-kirkiren da matasa ke yi a gida Najeriya cikin abubuwan da za'a rika kallo a matsayin abin afanarwa ga 'yan kasa. Ya bayyana hakane a Abuja wajan wani taro na musamman. Yace tattalin arziki na habakane idan aka ta'allakashi akan kirkire-kirkire da fasaha.
Fârgaba Yayin Da Sarki Sanusi, Aminu Ado Bayero Suka Sanar Da Jagòrantar Sâllar Juma’a A Masallaci Ɗaya, Shin me zai faru?

Fârgaba Yayin Da Sarki Sanusi, Aminu Ado Bayero Suka Sanar Da Jagòrantar Sâllar Juma’a A Masallaci Ɗaya, Shin me zai faru?

Kano
DAGA: Abbas Yakubu Yaura Tsòro ya mamaye tsòhon birnin Kano yayin da sarakunan biyu da ke hamayya da juna – Sarkin Kano Muhammadu Sanusi II da aka dawò dashi da Tsohon Sarkin Kano Aminu Ado Bayero da aka tsige suka bayyana shirinsu na yin sallar Juma’a a babban masallacin Juma’a na fadar Sarkin. Majiyar mu ta rawaito cêwa tuni mai martaba Sarki Malam Muhammadu Sanusi II, wanda ke zaune a fadar, kuma kusa da Masallacin da ake fafatawa, ana sa ran zai jagoranci sallar Juma'a raka'a biyu. Mai martaba Sarki Muhammadu Sanusi II zai jagòranci Sallar Juma’a a babban masallacin fadar a matsayin sarkin birnin, kamar yadda sanarwar ta bayyana. Sanarwar mai dauke da sa hannun Danburan Kanò, Munir Sanusi Bayero, ta bayyana matsayar Maimartaba Sarkin Kanò Muhammadu Sanusi II zuwa Masallacin...
A yayin da shuwagabanni da ‘yan siyasar Najeriya basu damu ba, shugaban kasar Kenya yace shi ba mahaukaci bane, ba zai iya biyan Dala Miliyan 150 ya dauki hayar jirgin sama ba

A yayin da shuwagabanni da ‘yan siyasar Najeriya basu damu ba, shugaban kasar Kenya yace shi ba mahaukaci bane, ba zai iya biyan Dala Miliyan 150 ya dauki hayar jirgin sama ba

Siyasa
Shugaban kasar Kenya, William Ruto yace ba zai iya daukar hayar jirgin sama akan kudi dala Miliyan 150 ba ya dauki tawagarsa zuwa taro a kasar Amurka ba. Ya bayyana hakane a wajan wani taro da ya gudana a kasarsa. Ya bayyana muhimmancin yin tattalin kudin talakawa inda yace kuma ya kamata shi ya fara nuna alamar abinda yake kira akai, watau rashin almubazzaranci. A baya dai, shima shugaban kasar Kenyan an zargeshi da yin wadaka da kudin talakawa.
A kara yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu uzuri, duk matsalolin da ake fama dasu yanzu ya gajesu ne daga Gwamnatin Buhari>>Tsohon Gwamnan Kano Ganduje

A kara yiwa shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu uzuri, duk matsalolin da ake fama dasu yanzu ya gajesu ne daga Gwamnatin Buhari>>Tsohon Gwamnan Kano Ganduje

Siyasa
Shugaban jam'iyyar APC kuma tsohon Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya baiwa 'yan Najeriya hakuri inda yace su ci gaba da baiwa gwamnatin Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu uzuri. Yace matsalolin da ake fama dasu, Tinubu ya gajesu ne daga Gwamnatin tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari. Ganduje ya bayyana hakane a wajan taron kaddamar da wani Littafi kan cika shekara 1 da gwamnatin Bola Ahmad Tinubu ta yi akan mulki. Ganduje ya kara da cewa, matakaj da Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu yake dauka na kawo gyara aun fara nuna alamar nasara.

Maganin Kaikayin gaban mace

Magunguna
MAGANIN CIWON SANYI NA MATA DA WANDA MAZA SUKE DAUKA WAJEN SADUWA DA IYALAN SU, ALAMOMIN MACE MEDAUKE DA SANYI Jin Zafi Lokacin Jima i Kaikayin Gaba Fitar farin ruwa agaba Gushewar Shaawa Warin Gaba ALAMOMIN SANYI NA MAZA Kankancewar Gaba Saurin Inzali Kaikayin Matse matsi Kaikayin Gaba Gushewar Shaawa Da Sauransu. WATO ( INFECTIOS ) 1- A samu namijin goro guda 5, 2- a samu citta mai ashar (mai yatsu) guda 4, ko 5 3- a samu tafarnuwa guda 3 a ko 4 ajajjaga su, 4- lemon tsami guda 5. Yadda Za a Hada maganin infection, kaikayin gaba Sai ayanka su kanana Kuma a jajjaga su,Shikuma lemon tsamin ayanka shi amatsa ruwan acikin tukuya, Kuma ajefa bawon aciki atafasa su dukka. Atace kafin asha, idan kuma babu dadin sha to azuba zuma...
Nawane Farashin dala a yau, 31/05/2024, Darajar Naira ta fadi

Nawane Farashin dala a yau, 31/05/2024, Darajar Naira ta fadi

Nawa ne farashin dala a yau
Darajar Naira ta fadi a kasuwar canji ta gwamnati a jiya, Alhamis. Kwanaki 3 kenan a jere darajar Nairar na faduwa a kasuwar Gwamnati. A jiyan, an sayi dalar Amurka akan Naira N1,484.76 wanda hakan ke nuna Naira ta samu faduwar 145.2 idan aka kwatanta da farashin ranar Laraba na Naira N1329.65 akan kowace dala. Saidai a kasuwar 'yan Chanji, Nairar ta dan samu tagomashi na Naira 5, inda aka sayi dalar akan Naira N1,485.