Saturday, December 20
Shadow
Da Duminsa: Kasar Burkina Faso taqi sàkò sojojin Najeriya 11 data kama, Tàcè bata yadda kuskurene yasa suka shiga sararin samaniyarta ba da izini ba

Da Duminsa: Kasar Burkina Faso taqi sàkò sojojin Najeriya 11 data kama, Tàcè bata yadda kuskurene yasa suka shiga sararin samaniyarta ba da izini ba

Duk Labarai
Rahotanni daga kasar Burkina Faso sun bayyana cewa, kasar ta ki yadda ta sako sojojin Najeriya 11 data kama da jirginsu C-130. Rahoton yace kasar ta Burkina Faso ta dauke sojojin daga inda ta ajiyesu a baya inda a yanzu ta kaisu wani waje me matsanancin tsaro. Kasar ta Burkina Faso ta yi imanin cewa sojojin na daga cikin wanda suka hana juyin Mulki a kasar Benin Republic. Dan Jarida, Oseni Rufai ya bayyana cewa ya samu daga majiya me karfi cewa har zuwa yanzu Hukumomin Najeriya basu tuntubi kasar Burkina Faso kan sakin sojojin ba. Najeriya dai tace sojojin na kan hanyar zuwa kasar Portugal ne jirgin su ya samu tangarda suka sauka a Burkina Faso.
Ana rade-radin, Janar Christopher Musa ka iya maye Kashim Shettima a matsayin mataimaki Shugaba Tinubu a 2027

Ana rade-radin, Janar Christopher Musa ka iya maye Kashim Shettima a matsayin mataimaki Shugaba Tinubu a 2027

Duk Labarai
Rahotanni na yawo cewa, Sabon Ministan tsaro, Janar Christopher Musa ka iya maye gurbin mataimakin shugaban kasa, Kashim Shettima a matsayin mataimakin shugaban kasa a 2027 Wani me sharhi akan al'amuran yau da kullun ne na siyasar Najeriya ya bayyana hakan inda yace ya samu wannan labari ne daga wata majiya me karfi. https://twitter.com/ChinonsoCharl15/status/1999487323214610651?t=nx502zWrcwwmSnrHHNOx5A&s=19
Da Duminsa:Shugaba Tinubu ya amince a sake Bude Depot (Makarantar Horas da sojoji) a Abakaliki

Da Duminsa:Shugaba Tinubu ya amince a sake Bude Depot (Makarantar Horas da sojoji) a Abakaliki

Duk Labarai
Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya amince a sake bude wata Depot watau makarantar horas da sojoji a Bakaliki dake jihar Ebonyi. Shugaban sojojin Najeriya, Lt. General Waidi Shuaibu ne ya bayyana haka a Zaria wajan yaye sabbin kurtan sojoji guda 3,439 da aka yi ranar Asabar. Yace wannan bude sabon depot zai baiwa sojojin damar daukar karin sojoji da zasu samar da tsari a Fadin Najeriya. Zuwa yanzu kenan yawan Depot din horas da sojoji da ake dasu a fadin Najeriya sun kai 3. Kaduna ⁠Osogbo ⁠Abakaliki
Kalli Bidiyon irin mùmmùnàr barnar da sojojin Najeriya sukawa Tshàgyèràn Dhàjì

Kalli Bidiyon irin mùmmùnàr barnar da sojojin Najeriya sukawa Tshàgyèràn Dhàjì

Duk Labarai
Sojojin Najeriya sun dakile wani yunkurin harin da 'yan Kungiyar ÌŚWÀP suka so kai musu a sansanin Forward Operating Base (FOB) dake Mairari. ÌŚWÀP sun so su afkawa sansanin sojojin da motoci 2 na yaki amma sojojin sun ankare dasu inda suka lalata duka motocin sannan suka jikkata tare da hallaqa wasu daga cikin maharan. Nasarar ta samu ne bisa hadin gwiwar sojojin sama sana kasa. Sannan daga baya sun bi daji inda suka ga gawarwakin 'yan Kungiyar da kuma kwato makamai. https://twitter.com/DejiAdesogan/status/1999788613236572535?t=pVncepIkEEmxZMuBs0SCHQ&s=19
Kalli Bidiyon: Wallahi da ka rayu a matsayin dan Darika ka koma ga Allah kana dan Darika, gara A halliceka a kàre, Ka rayu a kare kana hàùshì, ka kuma koma ga Allah a matsayin kàrè>>Inji Wannan malamin

Wannan malamin ya bayyana cewa, da ka rayu ka koma ga Allah a matsayin dan Dariqa, gara a halicceka a matsayin kare ka rayu kana haushi a matsayin kare sannan ka koma ga Allah a matsayin kare. Malamin ya bayyana hakane a wajan wani karatunsa wanda ya dauki hankulan mutane sosai. https://www.tiktok.com/@mohammedmhammed76/video/7582926715450559764?_t=ZS-92BdIKJ2kJU&_r=1
Kalli Bidiyon: Lokacin da na je zan gina Kamfanina, Akwai gidajen màtsàfà masu bautar gumaka guda 19 a wajan, Kuma saboda tsoronsu da ake, babu wanda ke iya zuwa wajan da suke

Kalli Bidiyon: Lokacin da na je zan gina Kamfanina, Akwai gidajen màtsàfà masu bautar gumaka guda 19 a wajan, Kuma saboda tsoronsu da ake, babu wanda ke iya zuwa wajan da suke

Duk Labarai
Attajirin Dan kasuwa, Aliko Dangote yace a lokacin da ya je zai gina matatar mansa, akwai gidajen Bokaye masu bautar gumaka guda 19 a wajan. Yace kowa tsoronsu yake babu wanda ke iya zuwa wajan. Yace Sarkin Yarbawa, Oni of Ife ne ya je wajan ya ce a rushe gidajen Bokayen. Dangote yace ba dan haka ba da ba zasu samu damar gina kamfanin nasu ba. https://twitter.com/yabaleftonline/status/1999482462121132313?t=LHeRuJTfaiUlCzz1GJhzZw&s=19