Wannan aikin na ciyar da kada abinci ana ganin kamar yafi kowane wahala a Duniya.
Ko nawa za'a baka ka iya yinshi?
https://www.youtube.com/watch?v=_5M-d07qjZk
Farashin dala ya dan fadi kasa a ranar Litinin, 27 ga watan Mayu na shekarar 2023.
An kulle kasuwar dalar akan ana sayen dala a farashin Naira 1,339.33.
Idan aka kwatanta da farashi Naira 1,482.81 da aka sayi dalar a ranar Juma'a, ana iya cewa an samu ci gaba.
Shugaban jam'iyyar ADC, Dr Ralphs Okey Nwosu ya bayyana cewa, sai an shekara 6 ana wahala kamin a kawo karshen wahalar da cire tallafin man fetur ya jefa mutane.
Ya bayyana hakane hirar da Daily Trust ta yi dashi.
Cire tallafin man fetur ya jefa mutane da yawa a cikin matsin rayuwa inda mutane suka rika fama da abinda zasu ci wanda a baya ba haka bane.
Saidai Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana cewa, wannan mataki ne data dauka dan amfanar al'umma baki daya wanda kuma na dolene.
Wasu alamu sun nuna cewa ga dukkan mai yiyuwa kwaikwakayar sa hannun babban alkalin kotun tarayya dake Kano aka yi aka fitar da hukuncin kotu na karya da yace a cire sarki Muhammad Sanusi II daga kan kujerar sarautar Kano.
A wani bincike da Kafar Daily Nigerian ta yi, ta gano cewa sa hannun da aka gani a takardar data dakatar da sarkin ta banbanta da sauran sahannun da alkalin ya saba yi.
Kuma a baya, Alkalin yakan saka hannu a duka takardun hukunci ne amma a na hukuncin da ya sauke sarkin, a takardar karshe ce kawai aka saka hannun.
Hakanan kuma Akwai wanda ake tuhuma a takardar kotun su 8 amma cikinsu babu wanda baiwa kwafin takardar sai kwamishinan 'yansandan jihar kadai.
Wannan yasa ake zargin cewa takardar ta boge ce.
Daga Imam Aliyu Indabawa
Tsohon Gwamnan jihar Sokoto Alhaji Attahiru Dalhatu Bafarawa ya yi Allah wadai da masu baiwa Buhari da gwamnatinsa kariya yana mai cewa duk mutumin da zai iya fitowa ya kare Buhari da gwamnatinsa to za su haɗu da shi a lahira a gaban Allah.
A yayin tattaunawarsa da kamfanin watsa labarai na BBC Hausa tsohon gwamnan ya ce," Bala'in da Buhari ya kawo ƙasar nan na lalacewar damokraɗiya da cin hanci ni dai a rayuwata ban taba ganin gwamnatin da ta kawo mana bala'i da masifa kamar ta Buhari ba."
Ya kuma nuna takaicinsa kan yadda gwamnatin Buhari ta ciyowa Nijeriya mummunan bashi na tiriliyoyi amma babu wani aiki da aka yi da kuɗin, ya ce wannan sai an je lahira za a yi shari'a a kansa.
Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya taya shugaban masa me ci murnar cika shekara guda akan mulki.
Ya bayyana hakane a wani sako da ya fitar.
Ya jawo hankalin mutane da su baiwa Tinubu goyon baya akan mulkin da yake yi.
Ya kuma yiwa Tinubun fatan kammala mulkinsa cikin nasara.
Dalibai mata da yawa a jami'ar University of Benin suna zargin wannan malamin me suna Anthony Asekhauno ya musu fyade.
Da yawansu sun hau shafukan sada zumunta inda suka rika bayyana yanda lamarin ya faru.
Wasu sun ce ya rika kayar dasu jarabawa da gangan dan ya samu damar yin lalata dasu.
Abin jira a gani shine matakan da hukumomi zasu dauka akanshi.
Kungiyar malaman jami'a ta ASUU ta yi barazanar shiga yajin aiki idan gwamnati ta kasa karawa membobinta Albashi da kuma inganta jami'o'in Najeriya.
Wakilan kungiyar na jami'o'in Akwa-Ibom, Uyo, University of Cross River State, University of Calabar, da University of Uyo ne suka bayyana haka.
Sunce rabon da a duba albashinsu dan kari shekaru 15 kenan duk da cewa sauran bangarori na kasarnan an kara musu albashin a lokuta da dama.
Sun kuma ce akwai alkawuran kudade da gwamnati ta musu wanda har yanzu bata cika ba.
Kungiyar tace amma ana hakane gwammatin ta dauki Biliyan 90 ta baiwa mahajjata a matsayin tallafi.
Wani mutum dan Najeriya ya bayyana cewa, idan aka sakashi wuta iri daya da ta tsohon ministan Sufurin Jiragen sama, Hadi Sirika ba'a masa adalci ba.
Mutumin ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumunta kuma ya fadi dalilinsa na cewa Hadi Sirika ya saci kudi da yawa.
Hadi Sirika dai na fuskantar tuhume-tuhume kan zargin satar Biliyoyin Naira da suka hada da biliyan 2 wanda ake zargin ya sata shi da diyarsa da surukinsa da kuma Biliyan 19 wadda ake zargin ya sata tare da kaninsa.