Wednesday, January 8
Shadow
BABU INDA DANGIN MIJI SUKA TAƁA SAKIN MATA DAN HAKA AMINU ADO YA DAWO KUJERARSA, CEWAR RASHEEDA MAISA’A

BABU INDA DANGIN MIJI SUKA TAƁA SAKIN MATA DAN HAKA AMINU ADO YA DAWO KUJERARSA, CEWAR RASHEEDA MAISA’A

Duk Labarai, Kano, Rashida Mai Sa'a
Fitacciyar jaruma a masana’antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood, kuma tsohuwar mai baiwa Ganduje shawara, Rasheeda Adamu Abdullahi Maisa’a ta bayyana cewa har yau Aminu Ado Bayero shi ne halastaccen sarkin Kano kuma ya dawo kujerarsa domin babu inda dangin miji suka taɓa sakin mata saboda ba su ne suka aura masa ita ba. Jaridar Dokin Karfe TV ta jiyo tsohuwar hadimar ta Ganduje wato Rasheeda Adamu Abdullahi Maisa’a na cewa yanzu haka Aminu yana Nasarawa kuma za su ɗau wanka su fita Ido yana gani su raka shi fadarsa batare da zare Ido ba. “Sarki Aminu mutum ne mai tsoron Allah har zuci ba a baki ba. Kuma ba a taɓa sarki mai haƙurinsa ba, ba ya tsoma baki da katsalandan cikin siyasa”. Mai Sa’a ta kuma ƙara da cewa Sarki Aminu bai zo Kano don ya tada tarzoma ba, domin ya san muhim...
Yanzu-Yanzu: Yaki ya barke tsakanin sojojin Israela dana kasar Misra/Egypt

Yanzu-Yanzu: Yaki ya barke tsakanin sojojin Israela dana kasar Misra/Egypt

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Yakin gaza da isra'ila
Rahotanni da muke samu daga gabas ta tsakiya na cewa, yaki ya barke tsakanin sojojin kasar Israela dana Misra/Egypt. Lamarin ya farune a daidai Rafah, kaamar yanda kafar Aljazeera ta ruwaito. A baya dai dama kasar ta Misra/Egypt ta gargadi Israela kada ta kai sojojinta yankin Rafah, saidai Israela ta yi kunnen uwar shegu da wannan gargadi indaa ta kai sojojin nata wajan. Biyo bayan hakan itama Misra/Egypt ta jibge sojojinta a iyakarta ta Rafah. To a yanzu dai yaki ya barke kamar yanda muke samun bayanai. Rahoton yace sojojin Misra/Egypt ne suka fara budewa na Israela wuta inda suma na Israelan suka mayar da martani. Saidai zuwa yanzu dai babu rahoton jikkata ko kuma rasa rai.
Muhammad Sanusi II ya goyi bayan zalunci a Kaduna>>Inji Shehu Sani

Muhammad Sanusi II ya goyi bayan zalunci a Kaduna>>Inji Shehu Sani

Duk Labarai, Kaduna, Kano
Tsohon sanatan Kaduna ta tsakiya, Sanata Shehu Sani ya bayyana cewa, me martaba sarkin  Kano, Muhammad Sanusi II ya goyi bayan zalunci a jihar Kaduna. Sanata Sani ya bayyana hakane a shafinsa na sada zumuntar Twitter. Sani yace Sarki Muhammad Sanusi II yana yakar zalunci a jihar  Kano amma kuma a baya ya goyi bayan zaluncin a jihar Kaduna. Sarki Sanusi dai abokine a wajan Tsohon Gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasiru Ahmad El-Rufai kuma a lokacin da aka cireshi daga mukamin sarkin Kano, ya koma Kaduna inda El-Rufai ya bashi waje ya bude fada sannan kuma ya bashi mukami a jami’ar jihar Kaduna.
Da Duminsa: Sheikh Dahiru Bauchi yayi magana akan dambarwar Sarautar Kano

Da Duminsa: Sheikh Dahiru Bauchi yayi magana akan dambarwar Sarautar Kano

Duk Labarai, Kano
Biyo bayan dambarwar data sarkake masarautar Kano, Babban malamin Addinin Islama, Sheikh Dahiru Bauchi ya fitar da sanarwa. Sheikh Dahiru Bauchi ta hannun gidauniyarsa, ya bayyana cewa yana baiwa Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf Shawarar kada yayi abinda zai kawo hargitsi a jiharsa ta Kano. Malamin ya bayyana cewa, bai ji dadin abinda gwamnatin jihar Kano ta yi ba na sauke Aminu Ado Bayero ta nada Muhammad Sanusi II ba. Ya jawo hankalin gwamnatin jihar ta Kano cewa, ta yiwa doka biyayya dan zaman lafiya me dorewa a jihar ta kano. Shugaban gidauniyar ta Dahiru Bauchi, Ibrahim Dahiruin ya bayyana cewa, babu wanda yafi karfin doka. Yayi kira ga majalisar majalisar tarayya da ta yi doka da zata hana ‘yan siyasa amfani da damarsu wajan wulakanta sarakai ta hanyar saukesu. ...
DA DUMI-DUMI: Kotu ta haramtawa Aminu Ado Bayero cigaba da bayyana kansa a matsayin Sarkin Kano, ta umurci yan sanda su fitar dashi daga fadar Nasarawa da yake ciki yanzu

DA DUMI-DUMI: Kotu ta haramtawa Aminu Ado Bayero cigaba da bayyana kansa a matsayin Sarkin Kano, ta umurci yan sanda su fitar dashi daga fadar Nasarawa da yake ciki yanzu

Duk Labarai, Kano
DA DUMI-DUMI: Kotu ta haramtawa Aminu Ado Bayero cigaba da bayyana kansa a matsayin Sarkin Kano, ta umurci yan sanda su fitar dashi daga fadar Nasarawa da yake ciki yanzu. Abin jira dai a gani shine ko ‘yansandan zasu bi umarnin Kotun, ganin cewa a baya ma an samu wata kotu ta bayar da umarnin hana sauke Aminu Ado Bayero amma umarnin bai yi amfani ba? Rigimar sarautar Kano dai ta dauki hankula sosai a kasarnan inda a karon farko aka samu sarakuna biyu a jihar da kowane ke cewa shine sarkin Kano.