Rikicin cikin gida ya kunno kai a kungiyar Izala.
Malam Ibrahim Matayassara ne ya fito ya ce yana jawo hankali ga Farfesa Sheikh Sani Rijiyar Lemu da cewa ya rika girmama malamai na zamaninsa ya daina tunanin shine ya fi owa ilimi.
Sannan Yace shi fadakarwa ce yayi ga Sheikh Rijiyar Lemu ba rashin kunya ba.
https://www.tiktok.com/@isah_bello_assalafy_garo/video/7563743936150310164?_t=ZS-90m2FmtZd9l&_r=1
Saidai lamarin ya jawo cece-kuce inda wasu malamai suka fito suka yi Allah wadai da wadannan kalamai nasa
https://www.tiktok.com/@sheikmurtala01/video/7564029374526196999?_t=ZS-90m1xKLFhJo&_r=1
Bidiyo ya bayyana inda aka ga yanda akawa Maiwushirya da 'YarGuda Gwaji a Asibiti a ci gaba da shirin aurensu.
https://www.tiktok.com/@pharooq_/video/7564102158837091604?_t=ZS-90m17FI9oP3&_r=1
Hakanan an ga sun je ofishin shugaban Hisbah na Kano, Malam Aminu Ibrahim Daurawa inda ya fati matakan da za'abi a kai ga auren.
Kotu dai tace nan da kwana 90 za'a daura auren.
Bidiyon abin kunyar da ya faru a jihar Ogun na ta yawo a kafafen sadarwa inda aka ga 'yan Najeriya na rokon 'yan kwallon kafar kasar Africa ta Kudu abinci.
'Yan kwallon wanda suka je filin kwallo na MKO Abiola dake Abeokuta dan wasa da Remo Stars sun rika jefawa 'yan Najeriyar sauran abincin da suka ci suka rage.
Da yawa dai sun yi Allah wadai da mutanen.
Kalli Bidiyon anan
https://www.youtube.com/watch?v=cq1Y4xEJEDo?si=MlWRJFlqZGtx8RYH
Tsohon shugaban kasa, Janar Olusegun Obasanjo me ritaya tare da dansa, Brigadier General Adeboye Obasanjo kenan a wannan hoton.
Hoton ya dauki hankula a kafafen sada zumunta inda akai ta sam barka
Tauraruwar Tiktok, Habiba Dorayi ta fito ta bayar da hakuri game da Bidiyon ta na batsa da ya watsu sosai a kafafen sada zumunta.
Habiba a Bidiyon data wallafa a shafinta na Tiktok tace hukumar tace fina-finan Kano ta nusar da ita cewa abinda ta yi bai dace ba.
Tace dan haka tana baiwa duk masoyanta hakuri kuma hakan ba zai sake faruwa ba.
Dan Najeriya, Mohammed Aminu Sani ya samu lasisin tuka hirgin saman Fasinja a kasar Amurka.
Hakan yasa ya zama matukin jirgin sama mafi karancin shekaru a Najeriya.
Matashin ya kammala makarantar horas da matuka jirgin sama dake Daytona Beach, Florida cikin watanni 10.
Da yawa na ta yaba masa.
Rahotanni sun ce a karin farko an ga Sauro a kasar Iceland.
Kasar Iceland dai itace daya tilo da babu sauro a Cikin a tsakanin kasashen Duniya.
Dalili kuwa shine kasar na da tsananin sanyi wanda sauro baya iya rayuwa a ciki.
Sannan kuma basu da ruwa dake kwanciya sosai wanda shima hakan na taimakawa wajan tara sauro.
Saidai duk da haka gashi a karin farko a yanzu an ga sauro a kasar.
Malam Nura Khalid ya bayyana cewa, mafi yawancin abinda zai kai mutanen Arewacin Najeriya wuta, hakkin bayin Allah ne.
Malam ya kawo misali da hakkin 'ya'ya akan iyaye inda ya kawo misalin masu haihuwar 'ya'ya su barsu suna watangaririya a titi.
https://www.tiktok.com/@digital_imaam/video/7563977265688710407?_t=ZS-90ld9ZHi77Z&_r=1