Thursday, December 18
Shadow
Da Duminsa: Ji yanda aka Yi cacar baki kiris ya rage a naushi juna tsakanin Godswill Akpabio da Sanata Opeyemi Bamidele a majalisar Dattijai

Da Duminsa: Ji yanda aka Yi cacar baki kiris ya rage a naushi juna tsakanin Godswill Akpabio da Sanata Opeyemi Bamidele a majalisar Dattijai

Duk Labarai
Rahotanni sun bayyana cewa, a jiya Laraba an samu wata dambarwa tsakanin kakakin majalisar Dattijai, Sanata Godswill Akpabio da sanata Opeyemi Bamidele. Muhawarar tasu ta yi zafi sosai ta yanda kiris ya rage su gwabza. Hakan ya farune a yayin da ake zaman taron shuwagabannin majalisar wanda suke tattauna ko su tafi hutu da suka saba tafiya ko kuwa a'a. A yayin zaman, Sanata Ali Ndume ya soki shugabancin Sanata Godswill Akpabio wanda hakan yasa shima sanata, Opeyemi Bamidele ya tashi yace shima bai jin dadin shugabancin Akpabio. Akpabio ya tashi tsaye yana cewa, shine shugaban majalisa kuma babu wanda ya isa yayi magana idan yana magana. Ya kuma kare kanshi bisa zargin da ake masa inda yace yasan aiki sosai yayi kwamishina yayi gwamna sau biyu, yayi babban minista yayi shugab...
Ba zai yiyu Mutum yana PDP kuma yace yana tare da hadakar jam’iyyar ADC ba, saidai mutum ya zabi daya>>Inji Gwamnan Bauchi

Ba zai yiyu Mutum yana PDP kuma yace yana tare da hadakar jam’iyyar ADC ba, saidai mutum ya zabi daya>>Inji Gwamnan Bauchi

Duk Labarai
Gwamnan jihar Bauchi, Sanata Bala Mohammed ya bayyana cewa ba zai yiyu mutum yace shi dan PDP ne kuma dan jam'iyyar hadaka ta ADC ne a saidai mutum ya zai daya. Gwamnan ya bayyana rashin jin dadinsa da 'yan jam'iyyar PDP dake hada kai da 'yan ADC. Yana maganane a wajan taron jam'iyyar ind yace ba zasu amince da rashin da'a ba dolene mutum ya zabi daya ko ADC ko PDP. Gwamnan yace hadakar ADC ba akan daidai suke ba.
Ya Kamata Shugaba Tinubu Ya Fitar Da Bayani Kai Tsaye Kan Zargin Sauya Shettima, Inji Baba Ahmad

Ya Kamata Shugaba Tinubu Ya Fitar Da Bayani Kai Tsaye Kan Zargin Sauya Shettima, Inji Baba Ahmad

Duk Labarai
Ya Kamata Shugaba Tinubu Ya Fitar Da Bayani Kai Tsaye Kan Zargin Sauya Shettima, Inji Baba Ahmad Daga Muhammad Kwairi Waziri Baba-Ahmed ya bayyana cewa Shugaba Bola Tinubu ya kamata shi da kansa ya fito ya musanta zargin da ake yi na shirin sauya mataimakin shugaban ƙasa, Kashim Shettima. Ya ce hakan zai taimaka wajen kwantar da hankulan jama’a da kawo karshen jita-jita marasa tushe. Ya kara da cewa, idan Shugaba Tinubu ya yi wannan bayani kai tsaye, zai nuna gaskiya da jajircewa wajen tafiyar da mulki cikin kwanciyar hankali da tsari.
Kananan yara 3 sun rigamu gidan gaskiya yayin da suke wanka a rafi a jihar Bauchi

Kananan yara 3 sun rigamu gidan gaskiya yayin da suke wanka a rafi a jihar Bauchi

Duk Labarai
Rahotanni daga jihar Bauchi na cewa wasu yara 3 dake wanka a wani rafi dake kauyen Jinkiri na karamar hukumar Bauchi a jihar Bauchi sun rigamu gidan gaskiya. Kakakin 'yansandan jihar, Ahmad Wakili ya tabbatar da faruwar hakan ga manema labarai ranar Laraba a Bauchi. Ya bayyana sunaye da shekarun yaran da suka rasu kamar haka: Habibu Mohammed, 16, Abubakar Mohammed, 16, da Zailani Sule, 14, yace dukansu sun fito ne daga kauyen Durum. Kuma sun rasu ranar Lahadi da misalin karfe 1 na rana. Yace yaran na aikin hakar ma'adanai ne kamin zuwa su yi wanka, yace an yi kokarin kaisu asibiti amma akan hanya suka rasu kamin a karasa. Yace likitoci sun tabbatar da mutuwar yaran kuma ana shirin mikasu wajan danginsu dan su binnesu.
Duk macen data san tana bin maza, yanzu an kawo sabon inji me gano maza nawa ta yi ma’amala dasu>>Murja Kunya

Duk macen data san tana bin maza, yanzu an kawo sabon inji me gano maza nawa ta yi ma’amala dasu>>Murja Kunya

Duk Labarai
{"remix_data":[],"remix_entry_point":"challenges","source_tags":[],"origin":"unknown","total_draw_time":0,"total_draw_actions":0,"layers_used":0,"brushes_used":0,"photos_added":0,"total_editor_actions":{},"tools_used":{"square_fit":1},"is_sticker":false,"edited_since_last_sticker_save":true,"containsFTESticker":false} Tauraruwar Tiktok, Murja Kunya ta bayyana cewa, yanzu sabuwar masifa ta bullo inda aka kawo sabon inji me gano mace maza nawa ta yi alfasha dasu. Mata masu bin maza yanzu ba sauran boye-boye: https://www.tiktok.com/@murjakunya0/video/7530366357129399560?_t=ZM-8yI0oXoCSxh&_r=1