Monday, March 2
Shadow
Kalli Bidiyon: Rahama Sa’idu ta sake bude babban Shago a Abuja

Kalli Bidiyon: Rahama Sa’idu ta sake bude babban Shago a Abuja

Duk Labarai
Tauraruwar Tiktok, Rahama Saidu ta sake bude babban shago Abuja. Rahama Sa'idu ta sanar da bude shagon nata ne a shafinta na sada zumunta inda aka ga 'yan uwa da abokan arziki ciki hadda mahaifinta sun halarci wajan bude shagon. https://www.tiktok.com/@rahamasaidu2/video/7549712291843837202?_t=ZS-8ziLVPQaxtp&_r=1 Tuni dai da yawa sukai ta mata fatan Alheri ana Allah san barka. https://www.tiktok.com/@rahamasaidu2/video/7549594929803152647?_t=ZS-8ziMBgVk9ez&_r=1
Allah Sarki: Yunusa Ahmadu Yusuf kenan wanda aka fi sani da Buhun Barkono da ya rigamu gidan gaskiya bayan ya shiga dakin Ota da wata me suna Ruth a Abuja

Allah Sarki: Yunusa Ahmadu Yusuf kenan wanda aka fi sani da Buhun Barkono da ya rigamu gidan gaskiya bayan ya shiga dakin Ota da wata me suna Ruth a Abuja

Duk Labarai
Yunusa Ahmadu Yusuf kenan wanda aka fi sani da Buhun Barkono wanda ya rasu a dakin Otal bayan ya shiga shi da wata me suna Ruth. Lamarin ya farune a ranar 8 ga watan Satumba inda bayan sun shiga dakin Yunusa Bai cin abinci saidai yayi ta kwankwadar giya, Kamar yanda rahotonni suka tabbatar. Ruth ta samowa Yunusa maganin kara karfin kuzari wanda bayan da ya sha ne ya suma daga nan kuma sai ya rasu. Tuni aka tafi dashi asibiti dan biciken abinda ya kasheshi. https://twitter.com/DejiAdesogan/status/1966940919791301113?t=zNsWv0rCyXZIrmev5QWxSA&s=19 Lamarin ya farune a Karu-Jikwoyi, Abuja.
Shugaba Tinubu ya cire tallafin man fetur ne saboda ci gaban Najeriya ba tare da damuwa ko za’a sake zabensa ba a 2027>>Inji Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila

Shugaba Tinubu ya cire tallafin man fetur ne saboda ci gaban Najeriya ba tare da damuwa ko za’a sake zabensa ba a 2027>>Inji Shugaban ma’aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila

Duk Labarai
Shugaban ma'aikatan fadar shugaban kasa, Femi Gbajabiamila ya bayyana cewa, Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya cire tallafin man fetur ne dan ci gaban Najeriya. Yace shugabab ya yi hakane ba tare da damuwa ko za'a sake zabensa a shekarar 2027 ba. Ya bayyana hakane a wajan wani taron tsaffin 'yan majalisar tarayya daga kudancin Najeriya wanda ya faru a jihar Ogun. Yace tabbas cire tallafin ya kawo wahalhalu amma na dan lokacine. Ya luma kawo misalai irin na tallafin karatun dalibai da sauransu wadanda suka taimaka wajan inganta ilimi da saukaka radadin da mutane ke ji.
Dubu 13 Gwamnan jihar Kebbi ke biyan malaman makarantar Firamare a matsayin Albashi>>Inji Dan Bello

Dubu 13 Gwamnan jihar Kebbi ke biyan malaman makarantar Firamare a matsayin Albashi>>Inji Dan Bello

Duk Labarai
Shahararren me yiwa 'yan siyasa Tone-tone, Dan Bello ya bayyana cewa, Naira 13,500 gwamnan jihar Kebbi ke biyan ma'aikata a matsayin mafi karancin Albashi. Yace hakan na zuwane a yayin da gwamnan zai kashe Naira Biliyan 1.3 a matsayin kudin sayen firjin. Naira 70,000 ne dai mafi karancin Albashi a Najeriya. https://twitter.com/BelloGaladanchi/status/1966876330127155307?t=m8xKKQI9CTnxwv27RY0L3g&s=19
Farashin kayan Abinci ya fadi kasa sosai>>Inji Gwamnatin Bola Ahmad Tinubu

Farashin kayan Abinci ya fadi kasa sosai>>Inji Gwamnatin Bola Ahmad Tinubu

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta bayyana cewa, Farashin kayan abinci ya fadi kasa sosai biyo bayan matakan da ta dauka. Ministan Noma, Senator Abubakar Kyari ne ya bayyana hakan a hirar da aka yi dashi a Arise TV. Yace sun shigo da shinkafa ne dan karya farashinta ba dan saka Manoma asara ba, yace kuma shigo da shinkafar daga kasashen waje na wucin gadi ne. Yace Najeriya na da gibin kaso 15 cikin 100 na shinkafar da ake bukata, kuma itace suka shigo da ita dan cike wannan gibi.
Bidiyon yanda wani mutum me suna Yunusa Ahmadu Yusuf, ya rigamu gidan gaskiya bayan shiga dakin otal da wata me suna Ruth a Abuja

Bidiyon yanda wani mutum me suna Yunusa Ahmadu Yusuf, ya rigamu gidan gaskiya bayan shiga dakin otal da wata me suna Ruth a Abuja

Duk Labarai
Wani mutum me suna Yunusa Ahmadu Yusuf ya rigamu gidan gaskiya bayan shiga dakin Otal da wata mata me suna Ruth. Lamarin ya farune a Karu-Jikwoyi, Abuja inda mutumin me shekaru 47 ya mutu. Rahotanni sun ce tun bayah da ya shiga daki da matar bai ci komai ba sai giya yake ta kwankwada. Matar ta fita ta sayo masa lemun kara karfin kwanji inda bayan ya sha ne ya suma, daga nan ne kuma rai yayi halinsa. Tuni an fara binciken dalilin mutuwarsa. https://twitter.com/DejiAdesogan/status/1966940919791301113?t=dEzEalSqKYaSMXghKfQCRA&s=19
Kalli Bidiyo: Shinkafar da aka dafa a Tukunya mafi girma a Duniya ta yi yawa, saida aka rika bin mutane ana basu a bakin titi

Kalli Bidiyo: Shinkafar da aka dafa a Tukunya mafi girma a Duniya ta yi yawa, saida aka rika bin mutane ana basu a bakin titi

Duk Labarai
Hilda Baci data dafa shinkafa a Tukunya mafi girma a Duniya a Legas ta rika bin mutane bakin titi tana raba musu shinkafar. Hakan ya biyo bayan yawan da shinkafar ta yi duk da mutane kusan dubu 20 da rahotanni suka ce sun yi rijista dan zuwa wajan cin shinkafar https://twitter.com/Teeniiola/status/1966916664051855714?t=PWgg0PIZ2xD8JAaqtMobTg&s=19 A baya dai an ga Bidiyon Hilda Baci na rokon mutane cewa su je su ci shinkafar dan ba yadda zata yi da ita, ta mata yawa.
Kalli Bidiyon: Shinkafar da aka bamu bata dahu ba, kuma ba nama, Inji daya daga cikin wadanda suka halarci wajan dafa shinkafa a Tukunya mafi girma a Duniya a Legas

Kalli Bidiyon: Shinkafar da aka bamu bata dahu ba, kuma ba nama, Inji daya daga cikin wadanda suka halarci wajan dafa shinkafa a Tukunya mafi girma a Duniya a Legas

Duk Labarai
Daya daga cikin wadanda suka halarci wajan dafa shinkafar Hilda Baci wadda aka dafa a tukunya mafi girma a Duniya a Legas, yace shinkafar bata dahu ba. Yace shinkafar ta yi dadi amma bata dahu ba sannan babu nama a ciki. https://twitter.com/Teeniiola/status/1966910035990372469?t=FrqBV6waJxMTTuvIPzMLGQ&s=19