Wata mata ta kashe aurenta saboda rikicin kudin kwalliya da mijinta ya ki bata.
Wasu dai sun bayyana cewa zata yi dana sani inda wasu ke cewa ta yi daidai.
https://twitter.com/__leenaaa/status/1980861476865716315?t=ACUxPOulIZpsimyuo2ASGg&s=19
Wannan wata Budurwa ce da lamarin ta ya baiwa mutane da yawa tausai.
Wasu matasa matsafa da aka fi sani da Yahoo Boys ne suka dauketa suka kaita gida da niyyar aikata Alfasha da ita amma a karshe ashe tsafi zasu yi da ita.
An ga Bidiyon ta tana ta rokon su kada su Kashye ta amma suka aikata lahira? Suka cire mata kai, da gabanta da sauran wasu sassan jikinta.
A karshe dai asirinsu ya tonu an kamasu.
Danna nan dan kallon Bidiyon
Wannan wata Baturiya ce dake sayar da Awara.
Wani ne da ya sayi awarar a hannunta ya dauke ta hoto yake yadawa a kafafen sada zumunta.
Wasu dai sun ce basu yadda da ita ba 'yar Leken Asiri ce.
https://twitter.com/Asound_Limwa/status/1980216952628138209?t=OyNmdqvLVgV_nYlHUCA9Rw&s=19
Ƙungiyar malaman jami’o’in Najeriya ASUU ta dakatar da yajin aikin gargadi na tsawon makonni biyu da ta fara, inda ta bai wa gwamnatin ƙasar wata ɗaya domin ta magance buƙatunta.
Shugaban ƙungiyar, farfesa Chris Piwunayayin wata ganawa da manema labarai, ya ce ƙungiyar ta yanke shawarar dakatar da yajin aikin ne domin bai wa gwamnati dama ta nuna kyakkyawan niyya wajen tattauna matsalolin da suka shafi albashi da kayan aiki da inganta yanayin aiki a jami’o’in kasar.
Ƙungiyar ta ce abun da yasa suka janye yajin aikin shine gwamnati ta gabatar da matsayarta kan sabunta yarjejeniysar shekarar 2009 kuma da kiraye-kirayen da suka samu daga mutane da dama daga ƙasar domin sun janye yajin aikin.
Wannan ne ya sa ƙungiyar ta bai wa gwamnatin ƙasar wata ɗaya domin ta magance buƙatunta.
K...
Tauraron Tiktok, Gfresh Al-amin ya baiwa 'yan Tiktok dake zaune a Kano shawarar su bar garin.
Ya bayyana hakane a Bidiyon daya wallafa bayan sanar da shirin auren Maiwushirya da 'YarGuda.
Gfresh yace An fara yiwa maza auren dole inda yace ko ba zasu iya kama gida a Abuja ba ko Kadunane su koma da zama ya fiye musu.
https://www.tiktok.com/@gfreshfanpage/video/7563781078125710610?_t=ZS-90lCnk8mKbx&_r=1
Wata bazawara daga kudancin Najeriya ta baiwa matan aure shawarar su rike mazajensu da kyau inda tace rayuwar zawarci ba dadi.
Bazawarar me amfani da sunan @rhoda2369 a kafafen sada zumunta tace rayuwar aure akwai kalubale amma mata su daure, rabuwa ba itace mafita ba.
Tace zata baiwa mace shawarar kashe aurenta ne kawai idan ta samu labarin cewa, ana dukanta.
Ganin diyar Ministan kasar Iran dake kula da tabbatar da saka Hijabi ta saka riga wadda babu kafada a wajan bikinta ya jawo cece-kuce.
Bayyanar Bidiyon a kafafen sada zumunta ya jawo zazzafar Muhawara wanda hakan yasa wasu ke sukar Gwamnatin da munafurci.
Shi dai wannan Ministan na kusa ne ga shugaban Jamhuriyar ta Iran.
Sunan Ministan Ali Shamkhani kuma a baya shine sakataren Ayatollah Khamenei sannan shine shugaban kula da tabbatar da saka Hijabi a kasar, kamar yanda daily Mail ta ruwaito.
A Bidiyon an ganshi tare da diyarsa inda sauran manyan baki a wajan ke musu tafi.
Ana dai ganin wannan shigartata ta yi kalar ta kasashen turai wadda kasar Iran ke yaki da irij Al'darsu.
https://www.youtube.com/watch?v=lVOJ80OzOTo
Majalisar Dattijai ta nemi a karawa sojojin Najeriya Albashi musamman lura da yanayin tsadar rayuwa da kasarnan ke ciki.
Majalisar tace ya kamata a karawa sojojin dake sadaukar da rayuwarsu dan baiwa kasarnan kariya Albashi.
Hakannna zuwane kasa da sati daya da bayyanar rahotannin yunkurin juyin mulki da ke cewa an kama sojoji 16 dake da hannu a lamarin.
Tauraruwar fina-finan Hausa, Princess Mufida ta Kwana Casa'in ta wallafa wasu hotuna a shafinta na sada zumuntar Instagram wanda suka jawo cece-kuce sosai.
Hotunan dai sun nuna ta babu riga ko rigar mama wanda wasu suka rika cewa tsirara take.
Wasu kuwa sun rika fatan ganin hoton dukanshi.
Saidai Mufida a kasar Hoton ta rubuta cewa na AI ne amma duk da haka mutane na ta mata Allah wadai.
Rahotanni sun bayyana cewa, Kungiyar lauyoyin Najeriya, NBA ta fitar da matsaya game da auren 'YarGuda da Maiwushirya.
Kungiyar tace ta samu labarin auren wanda wata kotun Magistrate ta yi a Kano.
Tace babu wata kotu dake da hurumin tursasa mutum yayi aure saboda hakan take hakkin bil'adama ne saboda aure abune wanda mutum ke yi saboda akwai soyayya da fahimtar juna tsakanin masoyan.
Dan haka NBA tace tana neman a sake duba wannan hukunci dan tabbatar ba'a takewa wanda lamarin ya shafa ba hakkinsu.
Saidai Rahotanni sun nuna cewa, Maiwushirya da kanshi ne yace zai auri 'YarGuda inda itama ta amince da hakan.