Monday, March 24
Shadow
Jirgin kasa dake jigila tsakanin Kaduna zuwa Abuja ya taka tare da kashe yara mata tagwaye a jihar Naija

Jirgin kasa dake jigila tsakanin Kaduna zuwa Abuja ya taka tare da kashe yara mata tagwaye a jihar Naija

Duk Labarai
Jirgin kasan daya taso daga Abuja zuwa Kaduna ya kashe kananan yaran wanda tagwayene mata a karamar hukumar Tafa. Lamarin ya farune da misalin karfe 10 na safe ranar Asabar, kamar yanda jaridar The Cable ta ruwaito. Yaran, Hassana and Hussaina Baro shekarar su daya da watanni 6. Kakakin 'yansandan jihar Naija, Wasiu Abiodun ya tabbatar da daruwar lamarin. Yace yaran suna wasa ne akan titin jirgin kasan kamin lamarin ya faru.
Mayakan Kungiyar ISWAP sun kashe manoma 15 a jihar Borno

Mayakan Kungiyar ISWAP sun kashe manoma 15 a jihar Borno

Borno
Mayakan kungiyar ISWAP sun kashe manoma 15 a jihar Borno. Sun kashe masuntanne a karamar hukumar Kukawa i da kuma da yawa suka jikkata. Lamarin ya farune da misalin karfe 10:40 na dare yayin da masuntan ke shirin fara kamun kifi na dare. Mayakan na ISWAP sun isa wajan da masuntan suke suka zagayesu suka kuma bude musu wuta. Wata majiya ta bayyanawa Daily Trust cewa mayakan sun sacewa masuntan kifi da yawa. Wanda suka rasu kuma an binnesu kamar yanda addinin musulunci ya tanada. Saidai har yanzu akwai wanda suka bace ba'a san inda suke ba.
Hotuna:Sojojin kasar Nijar sun kama kasurgumin dan Bindigar nan, Kachalla Baleri

Hotuna:Sojojin kasar Nijar sun kama kasurgumin dan Bindigar nan, Kachalla Baleri

Tsaro
Sojojin kasar Nijar sun kama kasurgumin dan Bindiga, Kachalla Baleri. Masanin harkar tsaro, Zagazola Makama ne ya bayyana hakan inda yace an kamashine a Rouga Kowa Gwani. Baleri wanda dan Shinkafine ya addabi mutane a Zamfara, Sokoto da Maradi. Ya jagorancin kisan mutane da yawa da kuma garkuwa da mutane da yawa. Yana daya daga cikin na hannun damar Kachalla Bello Turji kuma shine mutum na 40 mafi hadari da sojojin Najeriya suke nema ruwa a jallo.
Hotuna: Matashi Ya Raba Litattafai Gudu Dubu Goma Kyauta Ga Dalibai Domin Taya Gwamna Abba Murna Cika Shekara Guda Akan Mulki

Hotuna: Matashi Ya Raba Litattafai Gudu Dubu Goma Kyauta Ga Dalibai Domin Taya Gwamna Abba Murna Cika Shekara Guda Akan Mulki

Duk Labarai
Matashi Ya Raba Litattafai Gudu Dubu Goma Kyauta Ga Dalibai Domin Taya Gwamna Abba Murna Cika Shekara Guda Akan Mulki Shugaban Gidauniyar Sharu Sarakin Kwankwasiyya free computer training, Hon. Sharu Saraki ya rabawa dalibai littafin kimanin dubu goma domin taya Mai girma Gwamnan Kano Eng. Abba Kabir Yusuf murnar cika shekara daya akan mulki. Sannan kuma gidauniyar ta sake daukar nauyin dalibai mata ilimin kwamfuta kyauta a gidaunyar dake kan titin Airport road kusa da gidan man Danmarna kwanar kotun No-Man's-land.
Har yanzu Ni Budurwace fil A Leda, Namiji be taba sanina ba>>Inji Alex Unusual ta BBNaija

Har yanzu Ni Budurwace fil A Leda, Namiji be taba sanina ba>>Inji Alex Unusual ta BBNaija

Nishadi
Tauraruwar BBNaija, Alexandra Asogwa wadda aka fi sani da Alex Unusual ta bayyana cewa, har yanzu bata rasa budurcinta ba. Ta bayyana hakane a shafinta na sada zumunta. Abin ya baiwa mutane mamaki ganin cewa shekarunta 28 kuma musamman a wannan zamanin da ake ciki. A baya an yi zargin cewa tana lalata da me wasan barkwanci, AY, amma ta fito ta karyata wannan zargi.