Yadda ake hirar soyayya a waya
Hmmm....
Lallai kina son ko kuma kana son ka iya hirar soyayya a waya ko?
To bari dai in fara da cewa, a mafi yawancin lokuta ba a koyata, yanayinkane ke sa budurwa ta soka ko ta kika, ko kuma saurayi ya soki ko ya kiki.
Idan budurwa na sonka, kusan duk abinda kayi daidai ne, hakanan shima saurayi idan yana sonki.
Saidai akwai shawarwari da zan baku da zasu sa ku iya hirar soyayya ta waya.
Yadda ake hirar soyayya a waya
Da farko dai ya kasance kana yawaita kuranta budurwarka.
Ka rika gaya mata irin kyan da take dashi, wane fim ne ake yayi a lokacin, wane labari me dadine ya faru a irin wannan yanayin, wane abune kake tunanin bata sani ba wanda kai ka sani da kuma kake tunanin zai birgeta?
Idan zaka gaya mata magana, ka rika hada mata da misali na zahiri wanda ya far...