Ƙaruwar bashin da Najeriya ke ci abin damuwa ne – Shugaban majalisar wakilai
Kakakin Majalisar Wakilai, Abbas Tajudeen, ya nuna damuwa kan yadda bashin Najeriya ya ƙaru zuwa Tiriliyan 149.39 a farkon 2025, kwatankwacin dala biliyan 97, wanda ya wuce iyakar kashi 40% da doka ta gindaya, inda ya kai 52% na GDP.
Abbas ya bayyana haka ne a taron shekara-shekara na ƙungiyar WAAPAC a Abuja, yana mai cewa hauhawar bashin na barazana ga dorewar tattalin arziki, tare da gargadin cewa rancen da ke tallafa wa cin hanci da ciyar da bukatu bai kamata a ci gaba da shi ba.
Ya ce dole rance ya kasance domin ayyukan raya kasa kamar hanya, lafiya, ilimi da masana’antu.
Abbas ya kuma bayyana shirye-shiryen Najeriya na jagorantar kafa tsarin sa ido kan bashin majalisun dokoki a Yammacin Afirka domin tabbatar da gaskiya da tsari.
Kakakin ya jaddada cewa Majalisa za ta tabba...








