Fitar da maniyi akai-akai na rage haɗarin kamuwa da cutar sankarar mafitsara – Masana
Fitar da maniyi akai-akai na rage haɗarin kamuwa da cutar sankarar mafitsara - Masana
Koodinetan Shirin Yaƙi da Cutar Sankara na Ƙasa, ƙarƙashin Ma’aikatar Lafiya da Walwalar Jama’a, Dakta Uche Nwokwu, ya bayyana cewa yawan fitar maniyyi na iya rage haɗarin kamuwa da cutar sankarar mafitsara ga maza.
Nwokwu ya bayyana haka ne a yau Lahadi a Abuja, yayin wata hira da Kamfanin Dillancin Labarai na Ƙasa, domin mayar da martani kan batun da ya karade a kafafen sada zumunta cewa maza suna buƙatar fitar da maniyyi sau 21 a wata domin guje wa cutar prostate.
Ya yi bayani cewa gudanar da wasu al'amurra na rayuwa, ciki har da yawan fitar maniyyi, na iya taimakawa wajen rage haɗarin kamuwa da cutar jejin mafitsara.
Yana nuni da wani babban bincike da aka gudanar a 2016, wanda aka wallafa...







