Tuesday, April 29
Shadow

Me ake nufi da wasa kwakwalwa

Ilimi
Wasa Kwakwalwa na nufin yin wani da zai sa ka yi tunani ko nazari wajan samar dashi. Ko kuma ka yi Tunani ko Nazari wajan warware wata matsala, hakan na iya zama a makaranta ko kuma a rayuwarka ta zahiri. Misalin Wasa kwakwalwa shine idan aka tambayeka jihohi Nawane a Najeriya?, Ko ace maka goma a tara da takwas a debe uku. Ko kuma ace maka idan aka hada ruwa da madara da zuma me zasu bayar? Ko ace maka baba na daka gemi na waje, watau Hayaki, ko ace maka ja ya fado ja ya dauka, watau dan fulani da kayan giginya. Da dai sauran su.
Me ake nufi da naso a hausa

Me ake nufi da naso a hausa

Ilimi
Naso na nufin likewar wani abu a jikin wani abu ko kuma bayyanar wani abu a jikin wani abu dalilin haduwarsa da wani Abu. Misali, idan ka zuba ruwan sanyi a cikin kofi, zai yi naso a jikin kofin ta baya inda zaka rika ganin kamar zufa a bayan kofin. Ko kuma idan ka samu rigar bakanike, zaka ga bakin mai ya manne a jikinta, wannan mannewar ita ake kira da Naso. Ko kuma idan gini yana kusa da ruwa, zaka ga kasan katangar ginin kamar ta jike, wannan ma naso ne. Ina fatan wadannan misalai dana baka sun sa ka fahimci ko kin fahimci me ake nufi da Naso a Hausa.
Ina ake buga kudin nigeria

Ina ake buga kudin nigeria

Kasuwanci, Tarihi
Kanfanin Nigerian Security Printing and Minting (NSPM) ne ke buga kudin Najeriya. Kuma kamfanin na zaunene a Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya. A baya dai akan kai Kwangilar buga kudin zuwa kasashen waje amma a zamanin Mulkin Shugaba Buhari, an buga kudin na Naira a Najeriya. Saidai a duk sanda aka buga sabbin kudi, 'yan Najeriya kan yaba inda wasu ke kalubalantarsu, musamman ma dai ta bangaren ingancin Kudin.
Majalisar Dinkin Duniya ta saka Kasar Israela cikin masu kisan kananan yara

Majalisar Dinkin Duniya ta saka Kasar Israela cikin masu kisan kananan yara

Labaran Falasdinawa, Labarin Yakin Gaza, Siyasa, Yakin gaza da isra'ila
Majalisar Dinkin Duniya ta saka kasar Israela cikin kasashe masu kisan kananan yara. Hakan ya biyo bayan kisan sa kasar kewa Falas-dinawa a zirin gaza. Wakilin Israela a Majalisar Dinkin Duniya, Gilad Erdan ne ya bayyana haka. Inda yace an sanar dashi matakinne ranar Juma'a. Hakanan ministan harkokin kasashen waje na kasar Israela, Katz ya bayyana cewa, zasu dauki mataki kuma wannan abu da majalisar ta yi zai canja dangantakar dake tsakaninsu da Israela.
Kalli Hoto: Sabuwar cuta dake yaduwa ta hanyar Jima’i ta bayyana

Kalli Hoto: Sabuwar cuta dake yaduwa ta hanyar Jima’i ta bayyana

Kiwon Lafiya
Wata cuta da aka kira da Ring worms dake yaduwa ta hanyar Jima'i ta bayyana. Cutar dai wadda irintace a karin farko da aka gani a jikin dan adam ta bayyana ne a jikin wani dan kasar Amurka. Mutumin dai dan Luwadi ne wanda kuma yaje kasashe daban-daban yayi lalata da maza masu yawa. Bayan da ya koma kasarsa ta Amurka ne sai aka ganshi da wannan cuta. Saidai masana kimiyyar lafiya sun ce kada mutane su tayar da hankali dan cutar bata kai matakin barazana ga sauran al'umma ba. Ko da dai cutar Kanjamau akwai wasu majiyoyi dake cewa daga wajan 'yan Luwadi aka fara samota, hakanan ta tabbata cewa masu Luwadi sun fi saurin kamuwa da cutar.
Sai nan da shekarar 2029 farashin kayan masarufi zai sauko a Najeriya>>IMF

Sai nan da shekarar 2029 farashin kayan masarufi zai sauko a Najeriya>>IMF

Siyasa
Hukumar bada lamuni ta Duniya, IMF ta bayyana cewa, sai nan da shekarar 2029 farashin kayan masarufi zasu sauko kasa. Tace ta yi hasashen farashin kayan masarufin zai sauko da kaso 15 cikin 100 nan da shekarar ta 2029. A yanzu dai, Alkaluman kayan masarufi a Najeriya sun kai maki 33.69 kamar yanda hukumar kididdiga ta kasa, NBS ta bayyana. Tun dai bayan cire tallafin man fetur da gwamnatin tarayya ta yi ne dai aka shiga tsadar rayuwa wadda har yanzu babu alamar zata kare. Ko da a jiya, saida Gwamnatin shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ta bayyana cewa, zata sake daukar matakai masu tsauri wanda ka iya kara jefa 'yan Najeriya cikin halin matsi. Saidai Gwamnatin tace wadannan matakai da take dauka kokarine na tada komadar tattalin arziki.
Yanzu-Yanzu: Gwamnatin tarayya ta bayyana Naira dubu sittin da biyu (62,000) a matsayin sabon tayin mafi karancin Albashi

Yanzu-Yanzu: Gwamnatin tarayya ta bayyana Naira dubu sittin da biyu (62,000) a matsayin sabon tayin mafi karancin Albashi

Duk Labarai
Gwamnatin tarayya ta bayyana Naira Dubu sittin da biyu a matsayin sabon tayinafi karancin Albashi ga kungiyar Kwadago. Hakanan Sabon rahoton ya bayyana cewa, kungiyar kwadago ta NLC ta sauko daga matsayin ta na cewa gwamnati ta biyata Naira dubu dari hudu da chasa'in da hudu(494,000) inda a yanzu tace a biyata Naira dubu dari biyu da hamsin(250,000). Tuni dai kungiyar kamfanoni masu zaman kansu ta amince da tayin na gwamnatin tarayya watau dubu 62,000.
DA ƊUMI-ƊUMI: Ba za mu iya biyan N60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ba>>Gwamnoni

DA ƊUMI-ƊUMI: Ba za mu iya biyan N60,000 a matsayin mafi ƙarancin albashi ba>>Gwamnoni

Siyasa
Gwamnonin jihohin kasar nan 36 sun ki amincewa da tayin Naira dubu 60 mafi karancin albashi da gwamnatin tarayya ta ga. Daraktar yada labarai da hulda da jama’a ta kungiyar gwamnonin Najeriya, NGF, Hajiya Halimah Salihu Ahmed ce ta bayyana hakan a wata sanarwa da ta fitar a yau Juma’a. A tuna cewa a ranar Litinin ne kungiyar kwadago ta Najeriya NLC da kuma kungiyar ‘yan kasuwa, TUC, suka shiga yajin aikin sai baba-ta-gani bayan sun ki amincewa da tayin N60,000 da gwamnatin tarayya tayi a matsayin mafi karancin albashi. Amma daga baya sun sanar da cewa za su sassauta yajin aikin na tsawon mako guda domin ba da damar tattaunawa da gwamnatin tarayya, wadda ta yi alkawarin kara albashin daga N60,000. Sai dai gwamnonin sun ce mafi ƙarancin albashi na Naira dubu 60 ba mai yiwuwa ba n...