Gwamna Abba Kabir Yusuf ya sha Alwashin daukar mataki akan Malam Lawan Triumph bayan da aka kai masa korafi akan kalaman da yayi kan Janabin Annabi(Sallallahu Alaihi Wasallam)
Wasu mazauna birnin Kano a arewacin Najeriya sun yi zanga-zangar lumana game da zargin malamin addini Sheikh Lawan Abubakar Triumph da kausasa kalamai kan Annabi Muhammadu (SAW).
Masu zanga-zangar sun dangana da farfajiyar gidan gwamnatin Kano, inda Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tarɓe su tare da yi musu jawabi.
A baya-bayan nan ne aka ga malamin a wani bidiyo yana musanta batun cewa haihuwar Annabi da kaciya, kamar yadda wasu litattafai suka ruwaito, ba karama ba ce saboda "ana iya haihuwar sauran mutane ma da kaciyar".
A cewar malamin, karama na nufin "wani abin al'ajabi da Allah yake bai wa annabawa su kaɗai". Kazalika, malamin ya ce ruwayoyin ba su inganta ba.
Gwamna Abba ya umarci masu ƙorafin da su kwantar da hankali, inda ya nemi su rubuto masa takardar koke a hukumance ta h...








