Tuesday, December 23
Shadow
Ji Bayani Dalla-Dalla: Shin waye zaiwa gawar marigayi Dantata Sallah a Madina?

Ji Bayani Dalla-Dalla: Shin waye zaiwa gawar marigayi Dantata Sallah a Madina?

Duk Labarai
A yayin da manyan mutane musaman daga jihar Kano suka hallara a Madina dan halartar jana'izar marigayi Aminu Dogo, Dantata. Ana tababar wanene zai yiwa marigayin sallar gawa? Wasu rahotanni sun ce marigayin ya bar wasiyyar tsohon sarkin Kano, Aminu Ado Bayero ya mai sallar gawa wanda tuni shima yana can Madina. Saidai Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf da Sarkin Kano, Muhammad Sanusi II duk suma suna can Madinan. Zuwa anjima zami samu bayani kan yanda ta kaya.
Kalli Bidiyon: Shima tsohon shugaban APC, Ganduje ya tafi Madina dan halartar jana’izar Dantata

Kalli Bidiyon: Shima tsohon shugaban APC, Ganduje ya tafi Madina dan halartar jana’izar Dantata

Duk Labarai
Rahotanni daga Madina na cewa, Tsohon shugaban jam'iyyar APC da tawagarsa sun isa birnin dan halartar jana'izar Marigayi Aminu Dantata. A cikin tawagar Ganduje akwai sanata Barau Jibrin da sauransu. Hakan na zuwane kwanaki kadan bayan saukar Ganduje daga shugabancin jam'iyyar APC. https://twitter.com/tudunwada__mi/status/1939767084486951292?t=xz6XVz4xauDslIATf5EErw&s=19 Sauran wanda suka tafi Madina sun hada da Gwamnan Kano, Abba Kabir Yusuf, Gwamnan jihawa, Umar Namadi, da sauransu. Akwai kuma tawagar shugaban kasa wadda ministan tsaro, Abubakar Badaru ya jagoranta. Tsohon Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero shima ya tafi Madinan.
APC ta saka Naira Miliyan 20 a matsayin kudin fom din takarar Sanata sannan Naira Miliyan 10 a matsayin kufin Fom din takarar dan majalisar wakilai

APC ta saka Naira Miliyan 20 a matsayin kudin fom din takarar Sanata sannan Naira Miliyan 10 a matsayin kufin Fom din takarar dan majalisar wakilai

Duk Labarai
Jam'iyyar APC ta saka Naira Miliyan 20 a matsayin kudin sayen fom din takarar sanata sannan ta sa Naira Miliyan 10 a matsayin kudin fom din takarar dan majalisar wakilai a zabukan cike gurbi da ake shirin yi. Hakan na kunshene a cikin takardar bayanan ya da za'a gudanar da zaben da jam'iyyar ta fitar ta hannun babban sakatarenta, Sulaiman Argungu. Fom din tsayawa takarar dan majalisar jiha kuwa an sakashi akan Naira Miliyan 2. Matasa dake tsakanin shekaru 25 zuwa 40 zasu samu ragin kaso 50 cikin 100 na kudin sayen fom din. Jam'iyyar tace tana sayar da fom din a ofishinta dake Wuse II, Abuja
An saka ranar da shugaba Tinubu zai mayar da gwamban Rivers, Simi Fubara kan kujerarsa ta Gwamna

An saka ranar da shugaba Tinubu zai mayar da gwamban Rivers, Simi Fubara kan kujerarsa ta Gwamna

Duk Labarai
Rahotanni na cewa, a watan Yuli ne shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai mayar da gwamnan Rivers, Simi Fubara kan mukaminsa. Hakanan itama majalisar jihar a wannan watanne ke tsammanin mayar da ita kan aiki. Hakan na zuwane bayan da aka yi sasanci tsakanin Fubara da Wike. A ranar 18 ga watan Maris ne dai shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya dakatar da Gwamna Fubara da 'yan majalisar jihar inda ya bayyana cewa sun samu bayanan sirri musamman game da fasa bututun man fetur a jihar kuma Gwamnan ya kasa magance matsalar.
Kasar Saint Lucia ta girmama shugaba Tinubu

Kasar Saint Lucia ta girmama shugaba Tinubu

Duk Labarai
Kasar Saint Lucia ta girmama shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu da lambar girmamawa mafi girma a kasar. Hakan ya farune yayin da shugaba Tinubu ke ziyarar aiki a kasar kuma an karramashi ne dan kokarinsa wajan kyautata zumunta tsakanin kasashen biyu. Ba kasafai kasar Saint Lucia ke baiwa kowa wannan kyautar karramawar ba wanda hakan ke nuna muhimmancin da shugaba Tinubu ke dashi a wajansu.
Matatar man fetur ta Fatakwal ta dawo aiki

Matatar man fetur ta Fatakwal ta dawo aiki

Duk Labarai
An barke da murna a Eleme dake Birnin Fatakwal na jihar Rivers bayan ganin wutar matatar man fetur dake garin na ci balbal. Lamarin ya farune ranar Lahadi, 29 ga watan Mayu na shekarar 2025, wasu rahotanni na cewa, ana gwajin matatar man fetur dinne. 'Yan kasuwar man fetur dake kusa da matatar sun ce alamace matatar man fetur din na daf da dawowa da aiki dan ana kwacin ta ne. Rahotanni sun ce fiye da dala Biliyan 1 ne gwamnatin tarayya ta kashe Akan gyaran matatar man fetur din tun daga shekarar 2021 zuwa yanzu.
Kalli Bidiyon yanda manomi ya tsinci jaririya sabuwar haihuwa da aka binne da ranta a jihar Kebbi

Kalli Bidiyon yanda manomi ya tsinci jaririya sabuwar haihuwa da aka binne da ranta a jihar Kebbi

Duk Labarai
Wani manomi a jihar Kebbi me suna Kabiru Kamba ya ce ya tsinci jaririya sabuwar haihuwa da aka binne da ranta amma bata mutu ba a gona. An binne jaririyar a gonarsa dake Kamba karamar hukumar Dandi dake jihar. Ya bayyana hakane ga tawagar hukumar yaki da cin zarafi ta jihar da ta kai masa ziyara gida. Kamfanin dillancin labaran Najeriya, NAN ya ruwaito cewa, tsohuwar babbar sakatariya a jihar, Hajiya Rafa’atu Hammani.ce ta jagoranci tawagar zuwa gidan Kabiru. Yace a ranar da lamarin ya faru ya je gona sai yaga kunya wadda bai san da ita ba kuma ta yi sama sosai Yace anan ya kira mutane suka tayashi suna tonawa sai suka ga jaririya. Yace sun sanar da 'yansandan kusa da gurin inda yace kuma ya dauki yarinyar zai rike kuma an yi sa'a ma matarsa ta haihu dan haka ba za'a sam...
An Samu Mace Ta Farko Da Ta Kai Matakin Farfesa A Bangaren Haɗa Magunguna A Arewacin Nijeriya

An Samu Mace Ta Farko Da Ta Kai Matakin Farfesa A Bangaren Haɗa Magunguna A Arewacin Nijeriya

Duk Labarai
An Samu Mace Ta Farko Da Ta Kai Matakin Farfesa A Bangaren Haɗa Magunguna A Arewacin Nijeriya. Jami'ar Ahmadu Bello Dake Zaria Ta Ɗaga Likkafar Hajia Hadiza Usman Ma'aji Zuwa Matsayin Farfesa Akan Haɗa Magunguna Na Clinical Pharmacy, Wadda Ita Ce Mace Ta Farko A Arewacin Najeriya Da Ta Kai Wannan Matakin. Wace Irin Fata Za Ku Yi Mata? Daga Jamilu Dabawa
WATA SABUWA: Bayan sarki Sunusi na II ya isa ƙasar Saudiyya tare tawagar gwamnan Kano yanzu haka kuma sarki Aminu Ado Bayero ya kama hanyar Saudiyya domin cika wasiyyar Marigayi Alh. Aminu Dantata na cewa idan ya rasu shine zai masa Sallah

WATA SABUWA: Bayan sarki Sunusi na II ya isa ƙasar Saudiyya tare tawagar gwamnan Kano yanzu haka kuma sarki Aminu Ado Bayero ya kama hanyar Saudiyya domin cika wasiyyar Marigayi Alh. Aminu Dantata na cewa idan ya rasu shine zai masa Sallah

Duk Labarai
Bayan sarki Sunusi na II ya isa ƙasar Saudiyya tare tawagar gwamnan Kano yanzu haka kuma sarki Aminu Ado Bayero ya kama hanyar Saudiyya domin cika wasiyyar Marigayi Alh. Aminu Dantata na cewa idan ya rasu shine zai masa Sallah. Cikakken rahoto na nan tafeA Dimokuraɗiyya