Zan tsaya takarar shugaban kasa a 2027 – Peter Obi
Zan tsaya takarar shugaban kasa a 2027 – Peter Obi.
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar Labour Party a zaben 2023, Peter Obi, ya tabbatar wa magoya bayansa cewa zai tsaya takarar shugaban kasa a zaben shekarar 2027, kuma ba zai yi fiye da wa’adi guda ba idan ya ci zabe.
Mista Obi ya bayyana hakan ne a cikin wata sanarwa da mai magana da yawun Peter Obi Media Reports, Ibrahim Umar, ya fitar a ranar Litinin a Abuja.
Tsohon dan takarar shugaban kasar ya tabbatar da cewa yana cikin tattaunawar kafa kawancen jam’iyyu, yana mai cewa burinsa shi ne ceton Najeriya daga halin da ta tsinci kanta.
“Ban taba shiga wata tattaunawa kan hadin gwiwar tikitin takara da kowa ba, har da Atiku,” inji shi.
“Idan za a samu wata yarjejeniya da za ta takaita wa’adin mulkina zuwa shekaru hudu...








