Wednesday, December 24
Shadow
Jami’an Tsaro Sun Mamaye Hedikwatar Jam’iyyar PDP A Abuja

Jami’an Tsaro Sun Mamaye Hedikwatar Jam’iyyar PDP A Abuja

Duk Labarai
DA ƊUMIƊUMINSA: Jami’an Tsaro Sun Mamaye Hedikwatar Jam'iyyar PDP A Abuja. Daga Muhammad Kwairi Waziri A safiyar yau Litinin, an jibge jami’an tsaro a hedikwatar jam’iyyar PDP da ke Wadata Plaza, Abuja, gabanin babban taron Kwamitin Zartaswa na Ƙasa (NEC) da aka shirya gudanarwa a yau. Jami’an ‘yan sanda, DSS da Civil Defence sun mamaye ko’ina a harabar ofishin jam’iyyar domin tabbatar da tsaro yayin taron, wanda ake ganin zai yanke muhimmiyar shawara kan makomar jam’iyyar da shugabancinta. Wata majiya daga cikin jam’iyyar ta bayyana cewa ana sa ran tattaunawa mai zafi kan shugabancin jam’iyyar na ƙasa, inda ake hasashen sauyin wasu muƙamai ko sabbin shawarwari game da tsarin PDP na gaba. Ana sa ran dattawan jam’iyyar, gwamnoni da wakilan PDP daga jihohi daban-daban za s...
Labarin cewa an cire George Akume wanda kiristane daga mukamin sakataren gwamnatin tarayya, an mayeshi da musulma, Hadiza Bala Usman ka iya jawo rikicin addini>>Inji Kungiyar Kiristocin Najeriya, CAN

Labarin cewa an cire George Akume wanda kiristane daga mukamin sakataren gwamnatin tarayya, an mayeshi da musulma, Hadiza Bala Usman ka iya jawo rikicin addini>>Inji Kungiyar Kiristocin Najeriya, CAN

Duk Labarai
Kungiyar kiristocin Najeriya, CAN reshen Arewacin Najeriya tace labarin karya da aka rika yadawa cewa an cire George Akume daga mukamin sakataren gwamnatin tarayya tare da mayeshi da Hadiza Bala Usman ka iya jawo rikicin addini a kasarnan. Shuhaban kungiyar, Rev. John Joseph Hayab ne ya bayyana haka a sanarwar da ya fitar ga manema labarai a Kaduna. Yace Cire George Akume daga mukamin sakataren Gwamnatin barazana ce kai tsaye ga kiristanci, inda yace George Akume na daya daga cikin wakilai kalilan na kiristoci a cikin gwamnatin tarayya. Yace wanda suka kirkiro labarin da yadashi sun yi ne da wata manufa ta kawo rikici musamman na addini, musamman ganin cewa dama su kiristoci suna sane da cewa ana nuna musu wariya musamman a mulkin gwamnatin musulim musulim. Yace dan haka suna k...
Tawagar Gwamnatin Tarayya Ta Isa Ƙasar Saudiyya Domin Gudanar Da Jana’izar Alhaji Aminu Ɗantata

Tawagar Gwamnatin Tarayya Ta Isa Ƙasar Saudiyya Domin Gudanar Da Jana’izar Alhaji Aminu Ɗantata

Duk Labarai
Tawagar Gwamnatin Tarayya Ta Isa Ƙasar Saudiyya Domin Gudanar Da Jana’izar Alhaji Aminu Ɗantata. Tawagar gwamnatin tarayya ta isa ƙasar Saudiyya domin gudanar da jana’izar fitaccen ɗan kasuwa, dattijo, Alhaji Aminu Ɗantata a birnin Madina, wanda ya rasu a ƙasar Dubai yana da kimanin shekaru 94 a Duniya, kamar yadda Dokin Ƙarfe TV ta ruwaito. Tawagar wadda ke ƙarƙashin jagorancin tsohon gwamnan Jihar Jigawa, kuma ministan tsaron ƙasa, Alhaji Muhammad Badaru Abubakar, ta haɗa da ministan shari’a Lateef Fagbemi SAN, da ministan yaɗa labarai da wayar da kai, Alhaji Muhammad Idris, da ƙaramin ministan gidaje, Yusuf Abdullahi Ata. Sauran ƴan tawagar sun haɗa da: manyan malaman addinin musulunci, Dakta Bashir Aliyu Umar, Shaik Aminu Ibrahim Daurawa da kuma Khalifa Abdullahi Muhammad,...
Tonon Silili: Ji yanda shugaba Tinubu ya tafi neman lafiya a asirce dan kada ‘yan Najeriya su mai surutu

Tonon Silili: Ji yanda shugaba Tinubu ya tafi neman lafiya a asirce dan kada ‘yan Najeriya su mai surutu

Duk Labarai
Rahotanni sun ce tafiyar da shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi zuwa kasar Saint Lucia da fadar shugaban kasar tace hanyace ta kulla alaka tsakanin kasashen biyu, dabara ce kawai ta neman lafiya da shugaban kasar ya fita yi. Rahoton yace Shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya yi amfani da kasar Saint Lucia ne dan neman magani inda maimakon a baya da yake zuwa asibiti, a wannan karin likitocin sa ne za'a dakko su dubashi a kasar. Rahoton wanda ya fito daga Sahara reporters wadda ita kuma tace ta samoshi ne daga wata majiya me tushe ta kusa da shugaban kasar tace, an yi hakanne dan kaucewa idon 'yan jarida kada su kwarmata cewa shugaban kasar ya je nema lafiyane. A baya dai shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu ya je neman lafiya kasashen waje wanda hakan yaci karo da suka daga 'yan Naje...
Da Duminsa: APC ta yi magana kan komawar Kwankwaso jam’iyyar

Da Duminsa: APC ta yi magana kan komawar Kwankwaso jam’iyyar

Duk Labarai
Jam'iyyar APC ta yi magana kan rade-radin dake jawo cewa Dr. Rabiu Musa Kwankwaso na shirin komawa jam'iyyar. Hakan na zuwane bayan da Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya ajiye mukaminsa a matsayin shugaban jam'iyyar APC inda ake ta samun rahotannin cewa, yanzu Kwankwaso zai koma jam'iyyar. Me magana da yawun jam'iyyar APC a hirar da aka yi dashi a gidan talabijin na Channels TV yace babu wannan maganar. Yace bai san komai ba game da rahotannin dake yawo cewa Kwankwaso zai koma jam'iyyar APC ba. A wasu rahotannin dai har cewa aka yi shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu zai dauki Kwankwaso a matsayin abokin takararsa.
Ji yanda Matasan jihar Anambra ke soyayya harma da aure dan kawai su rika haihuwar jarirai suna sàyàrwà

Ji yanda Matasan jihar Anambra ke soyayya harma da aure dan kawai su rika haihuwar jarirai suna sàyàrwà

Duk Labarai
Hukumar yaki da safarar mutane ta Najeriya, NAPTIP tace matasan jihar Anambra sun baci da dabi'ar sayar da jarirai. Kwamandar hukumar ta jihar, Ibadin Judith-Chukwu ce ta bayyana hakana wata sanarwa data fitar inda tace abin yayi yawa tsakanin matasa. Tace abin yafi kamari a kauyuka dan hakane suka kafa wata tawaga ta musamman dan yaki da wannan mummunar dabi'a. Ibadin Judith-Chukwu tace matashi zai yiwa yarinya ciki dai ya aureta amma tana haihuwar jaririn sai ya lalaba ya saceshi ya sayar bada sanin mahaifiyar ba. Tace amma suna ta kokarin wayarwa da mutane kai game da lamarin.
Tinubu Rahama ne ga Najeriya, Ya hana mutane da yawa mutuwa>>Inji Kungiyar kare muradin Yarbawa ta YCG

Tinubu Rahama ne ga Najeriya, Ya hana mutane da yawa mutuwa>>Inji Kungiyar kare muradin Yarbawa ta YCG

Duk Labarai
Kungiyar kare muradun yarbawa ta YCG ta bayyana shugaban kasa, Bola Ahmad Tinubu a matsayin shugaba na gari wanda rahama ne ga 'yan Najeriya. Kungiyar tace tsare-tsaren shugaba Tinubu sun taimaka wajan samar da tsaro, ga rayuwa da dukiyoyin jama'a. Kungiyar tace a cikin shekaru 2 da shugaba Tinubu yayi yana mulki, Gwamnatinsa ta samar da tsaro da kara karfin tattalin arzikin Najeriya. Wakilan Kungiyar Olugbemga Oyewusi, Mrs Buky Tunde Oshunrinde, ne suka bayyana hakan a sanarwar da suka fitar ga manema labarai. Sun ce Yabo Shugaba Tinubu ya cancanta ba barazana da zagi ba.
Gwamnan Kano ya jagoranci tawogar Kano da Jigawa zuwa halartar jana’izar Dantata a Madina

Gwamnan Kano ya jagoranci tawogar Kano da Jigawa zuwa halartar jana’izar Dantata a Madina

Duk Labarai
Gwamnan Kano ya jagoranci tawogar Kano da Jigawa zuwa halartar jana'izar Dantata a Madina. Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, ya tashi daga Filin Jirgin Sama na Malam Aminu Kano, inda yake jagorantar wata babbar tawaga domin halartar jana’izar fitaccen attajiri kuma dattijon kasa, marigayi Alhaji Aminu Alhassan Dantata, a birnin Madina mai alfarma, da ke Kasar Saudiyya. Marigayin ya rasu da safiyar Asabar a birnin Abu Dhabi na Hadaddiyar Daular Larabawa. Wannan bayanin na cikin wata sanarwa da mai magana da yawun gwamnan, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya fitar. Tawagar tana dauke da Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, Gwamnan Jihar Jigawa, Alhaji Umar Namadi, tsohon gwamnan Jigawa Barr. Ali Sa’ad Birnin Kudu, da wasu manyan jami’an gwamnati da fitattun dattawa...